Gwamatin Tarayya ta shirya kammala aikin madatsar ruwa ta Dasin Hausa a Adamawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta shirya kammala aikin madatsar ruwa ta Dasin Hausa dake jihar Adamawa.

Aikin, wanda aka dakatar tun a shekarun 1980s, zai magance matsalolin ambaliyar ruwan da ke fitowa daga madatsar ruwa ta Lagdo a Kamaru.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Hukumar ICRC da gwamati za su haɗa gwiwa da kamfanin Mainstream Energy don kammala aikin a kan lokaci, a ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP).

Kmmala Madatsar ruwan, zai taimaka wajen samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 300, kana ta bayar da damar noman rani a gonakin da suka kai hekta 150,000 a Jihohin Adamawa, Taraba da Benue, tare da kare dukiyoyin da kimarsu ta kai biliyoyin nairori daga ambaliya a duk shekara.

Baya ga haka, ana sa ran kammala madatsar zai farfaɗo da tattalin arziƙi da ƙarfafa gwiwar al’ummomin da ke yankin na kogin Taraba, Adamawa, Neja da Benue.

By Babaji