Yanomami: Ƙabilar da ke ƙone gawar danginsu su cinye

Ƙabilar Yanomami wanda aka fi sani da ‘Senema’ ko ‘Yanam’ da aka fi samu a yankunan ƙasashen Brazil da Venezuela, a Kudancin Amurka, tana da wata al’ada mai ban mamaki ta ƙone duk wanda ya mutu a cikinta ta sarrafa ta cinye.

’Ya’yan wannan ƙabila ba su damu da abubuwan zamani ba, sun fi mai da hankali ga ci gaba da bin al’adunsu na gargajiya.

Saɓanin yadda sauran ƙabilu ke binne mutum idan ya rasu, ƙabilar Yanomami ta bambanta na ƙonewa ne ta ci naman matacce, duk lokacin da ɗan uwansu ya mutu ko wani da ke zaune a yankunansu.

Ƙabilar Yanomami tana da aƙidar cewa akwai buƙatar a kare ran mutum ko bayan ya rasu, hakan kuma zai faru ne idan aka gasa ko ƙone gawarsa, kuma ’yan uwansa suka cinye naman.

Suna ƙonewa ko gasa gawar sannan su bar ƙasusuwan kaɗai, sai su daka ƙasusuwan su koma gari su haɗa da tokar gawar.

Sukan yi amfani da garin da suka daka su haɗa wata miya, wadda suke amfani da ita wajen yin maganin rashin lafiya na gargajiya inda ’yan uwan mamacin ne za su yi amfani da ita.

Sun amince da cewa idan har aka yi wa mamaci wannan al’adar tasu zai yi kwanciyar kabari cikin nasara da zaman lafiya.

Ba kamar yadda aka saba bikin binne mamaci ba, su ƙabilar Yanomami ’yan asalin ƙabilun Indiyawan Daji, sun kasance suna ƙone gawar mamaci sannan su yi wa fuskarsu fenti daga tokar gawar mamacin.

Sukan yi waƙa tare da kuka don nuna alhininsu ga rasuwar ɗan uwansu.

A wani ɓangare na al’adar Yanomami kuma, idan wani maƙiyi ya yi kisa ko aka kashe wani ɗan yankin ƙabilar, mata ne kaɗai za su cinye naman mamacin da yin amfani da tokar gawar.

Daga bisani za iya ramuwa a kan wanda ya aikata kisan sannan za a yi bikin al’ada a daren aka yi kisan, yayin da za a yi ramuwar kisan a yankin da aka yi shi.