Yanzu ’yan Nijeriya sun gane ku maƙaryata ne — Wike ya caccaki ADC da NDC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya soki jam’iyyun adawa kan rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓukan fidda gwani da tarukan jam’iyyunsu.

Wike ya ce rikice-rikicen da suka faru a jam’iyyun ADC da NDC sun nuna cewa ikirarin da suke yi na kawo sabon salo a siyasar Nijeriya ba gaskiya ba ne.

Da yake jawabi yayin tattaunawarsa da manema labarai a Abuja, Wike ya ce jam’iyyun adawar sun dade suna zargin manyan jam’iyyu irin su APC da PDP da tilasta wa ‘ya’yansu ‘yan takara.

Sai dai ya ce abubuwan da suka faru a cikin sabbin jam’iyyun sun nuna cewa su ma suna fama da matsalolin cikin gida da rashin adalci.

“Kullum za ka ji suna cewa wata jam’iyya tana yin abu ba daidai ba, kuma su idan sun zo za su gyara tsarin. Sun zargi APC da PDP da yin murdiya da kakaba ‘yan takara,” in ji Wike.

“Yanzu kuma sun kafa sabuwar jam’iyya, wai sabuwar jam’iyya mai tsarki, mai ceto. To me ya faru yanzu?”

Tsohon gwamnan Jihar Ribas ɗin ya yi nuni da rikice-rikicen da suka biyo bayan tarukan jam’iyyun ADC da NDC, yana mai cewa hakan ya rusa ikirarinsu na gaskiya da dimokuraɗiyya.

“ADC ta ce ita ce sabuwar fuskar dimokuraɗiyya, jam’iyyar da ba ta gurɓace ba. Amma abin da ya faru yanzu ya fi ƙazanta,” ya ce.

“Ku duba abin da ke faruwa a NDC. Duk da ƙanƙantarsu, sun kasa gudanar da zaɓen fid-da-gwani ba tare da zanga-zanga ba.”

Wike ya kuma yi magana kan koke-koken da wasu masu neman takara suka yi yayin zaɓukan, yana mai cewa hakan ya jefa shakku kan sahihancin tsarin.

Zaɓen fid-da-gwani na shugaban ƙasa na ADC dai ya fuskanci ce-ce-ku-ce bayan Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, suna zargin an tafka magudi da hana wasu kaɗa ƙuri’a.

“Ku duba ADC ɗin da ta ce haɗakar ce za ta karɓi mulki. Yayin da ake gudanar da zaɓen, ‘yan takarar shugaban ƙasa biyu suka fito suna cewa ba za su yarda da abin da ya faru ba, suna kiransa babban laifi. Wannan ya nuna wa mutane wa ke yaudarar wa,” inji shi.

Wike ya ce abubuwan da suka faru sun nuna cewa ya kamata ‘yan Nijeriya su dinga kallon ayyukan jam’iyyu maimakon kalaman yaƙin neman zaɓe kawai.

“Yanzu ‘yan Nijeriya sun gane cewa duk ku makaryata ne,” ya ƙara da cewa.

Ministan ya kuma bayyana cewa tsofaffin jam’iyyun siyasa sun fi ƙwarewa wajen tafiyar da siyasar Nijeriya duk da matsalolin da suke fuskanta.

“A ganina, na fi son tsofaffin jam’iyyun da suka daɗe suna siyasa. Sun riga sun san yadda tsarin siyasar Nijeriya yake,” inji Wike.

By ukarofi