Babachir ya fice daga ADC bisa zargi Atiku da maguɗin zaɓen fidda gwani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC, inda ya zargi shugabannin jam’iyyar da tafka maguɗi a zaɓukan fidda gwani da aka gudanar domin amfanin Atiku Abubakar da magoya bayansa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Lawal ya ce an yi maguɗi a matakai daban-daban na zaɓen fidda gwani, yana mai cewa an maye gurbin wasu waɗanda suka yi nasara da mutanen da ke da alaƙa da Atiku.

A zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da ADC ta gudanar, Atiku ya samu ƙuri’u 1,846,370 inda ya doke Rotimi Amaechi wanda ya samu ƙuri’u 504,117, yayin da Mohammed Hayatu-Deen ya samu ƙuri’u 177,120.

Lawal ya ce ba zai shiga cikin duk wani shirin maguɗin zaɓe ba kafin zaɓen 2027, yana mai bayyana Atiku a matsayin wanda bai dace ya jagoranci ƙasa ba. Ya kuma yi alkawarin yin aiki domin hana Atiku samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Tun da farko, Amaechi da Hayatu-Deen sun yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na ADC tare da kaurace wa sanar da sakamakon a Abuja.

By ukarofi

Leave a Reply