‘Yan bindiga sun buƙaci a saki mutanensu da shanunsu kafin su saki Janar Rabe da matarsa a saƙon bidiyo

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Manjo Janar Abubakar Rabe (rtd) da matarsa ​​​​waɗanda aka sace a kan titin Karaɗuwa-Matazu a Jihar Katsina mako guda da ya gabata sun roƙi gwamnati da ta taimaka musu ta kuɓutar da su daga hannun waɗanda ke garkuwa da su.

‘Yan bindigar da ke garkuwa da su sun fitar da wani sabon bidiyo da ke nuna ma’auratan tsare a cikin daji.

A cikin bidiyon mai tsawon mintuna huɗu, da aka yaɗa a shafukan sada zumunta, an ga ma’auratan suna tsaye suna isar da buƙatun ‘yan bindigar, inda suka buƙaci a saki wasu abokan ta’addancinsu kafin su saki tsohon kakakin rundunar sojin tare da matarsa.

Da take magana a cikin bidiyon, matar janar ɗin soja ta isar da buƙatar masu garkuwar na sakin membobinsu uku da aka ambata a matsayin Sani, Aminu, da Nasiru.

Masu garkuwar sun kuma nemi a dawo da dabbobin da ake zargin an ƙwace musu.

A cikin bidiyon matar Janar Rabe ta bayyana cewa, an kama mutum biyu daga cikin mutanen da aka tsare a Jiƙamshi, yayin da aka kama na ukun a Kano.

Ta ƙara roƙon gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin ƙananan hukumomi biyar da su sauƙaƙa biyan buƙatun don a sake su.

Janar Rabe mai ritaya, wanda ya yi magana a taƙaice a cikin bidiyon, ya yi kira da a yi ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya, yana mai cewa masu garkuwar sun nuna sha’awar tattaunawa da kuma zaman lafiya a tsakaninsu.

A cikin bidiyon, ba a ambaci buƙatar fansa ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, Gwamnatin Jihar Katsina ko hukumomin tsaro ba su fitar da sanarwa a hukumance game da bidiyon da masu garkuwar suka fitar ba.

Rahotanni sun ruwaito cewa Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya yana tafiya zuwa Katsina a ranar Asabar tare da matarsa, Hajiya Amina Abubakar, da direbansu, Abdullahi Sa’idu, lokacin da aka yi wa motarsu kwanton ɓauna a kan titin Marabar Musawa-Kafinsoli a ƙaramar hukumar Matazu.

Harin ya faru ne kusa da ƙauyen Zakin Ɓaure, inda shaidu suka ce mutane ɗauke da makamai, waɗanda ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne, sun fito ba zato ba tsammani daga ɓuya, suka toshe hanya suka buɗe wuta a kan motar, lamarin da ya tilasta mata tsayawa.

Wata majiyar ta ce an harbi direban a hannu a lokacin harin amma bai mutu ba lamarin da yasa aka garzaya da shi zuwa asibiti.

Jaridar Manhaja ta rawaito cewa fitaccen shugaban ‘yan fashin daji dake addabar wasu sassan jihar Katsina, Kachallah Muhammadu, ya ce Janar Rabe yana hannunsu ya kuma yi iƙirarin cewa sun daɗe suna bibiyarsa kafin su kama shi tare da matarsa.

By ukarofi

Leave a Reply