Soja biyar da jami’an CJTF uku sun rasu yayin da dakarun tsaro suka daƙile harin ‘yan ta’adda a Borno

Spread the love

Dakarun tsaro na rundunar Atisayen HAƊIN KAI da ke sansanin Forward Operating a Mandaragirau a ƙarƙashin Brigade ta 25 sun dakile wani hari da ake zargin ’yan ta’adda ne suka kai da sanyin safiyar Juma’a a jihar Borno, bayan artabu mai tsanani da ya biyo bayan yunƙurin kutsawa sansanin a yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi.

Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ta ce dakarunta sun mayar da martani cikin gaggawa tare da hana maharan cimma manufarsu, lamarin da ya jawo asara ga ɓangaren ’yan ta’addan, duk da cewa ba a bayyana adadin waɗanda aka kashe ko suka jikkata ba.

Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa sojoji biyar sun rasa rayukansu yayin musayar wuta, yayin da jami’an rundunar sa-kai ta CJTF uku su ma suka mutu a fagen daga. Haka kuma an ce an kwashe waɗanda suka jikkata ta jirgin sama domin samun kulawar likita.

A cewar rundunar, dakarun tsaro na ci gaba da rike sansanin tare da gudanar da ayyukan sintiri da bincike a yankin domin tabbatar da tsaro da hana sake kai hare-hare.

Kodayake babu wata sanarwa daga ɓangaren da ake zargin ya kai harin, jami’an tsaro sun bayyana harin a matsayin wata alama ta ƙoƙarin da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ke yi na sake farfaɗowa duk da matsin lambar hare-haren soji a yankin Arewa maso Gabas.

By Babaji

Leave a Reply