
Kimanin mutane 49 ne suka rasa rayukansu sakamakon ƙishin ruwa da tsananin zafin rana bayan motarsu ta lalace a wani yanki mai nisa na hamadar sahara a Jihar Agadez da ke arewacin, Jamhuriyar Nijar.
Rahotanni sun bayyana cewa, matafiyan na dawowa ne daga Mali bayan halartar taron addinin Musulunci lokacin da suka maƙale ba tare da ruwa ko taimako ba.
Haka kuma, an ruwaito cewa mutane biyu ne kawai suka tsira bayan sun yi tafiyar sama da kilomita 50 a ƙafa domin neman agaji.
Hukumomi sun ce, an binne mamatan a kabari guda, yayin da jami’an ceto suka ceci wasu matafiya sama da 60 da suka maƙale a wani wuri daban a hamadar bayan sun kwashe kwanaki uku cikin yunwa da ƙishi.
Lamarin ya sake nuna irin haɗurran da ke tattare da zirga-zirga ta hamadar sahara, wadda ke ci gaba da haddasa asarar rayuka ga matafiya da masu ƙaura.
