
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi wa sanatocin da suka sha kaye a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC alƙawarin samun tikitin takara.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara akan harkokin yada labarai, Eseme Eyiboh ya fitar, Akpabio ya bayyana cewa abin da ya yi shi ne nuna tausayi ga sanatocin da sakamakon zaben fidda gwani ya shafa, tare da tabbatar musu cewa shugabancin APC na kokarin magance matsalolin da suka taso daga zaben.
Ya jaddada cewa ba zai tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar ba, kuma yana bin ka’idojin jam’iyya da tsarin doka.
Haka kuma, Akpabio ya ce yanzu ba lokaci ba ne da ya dace a gudanar da binciken jama’a kan ayyukan sojoji, yana mai cewa hakan na iya rage musu kwarin gwiwa a lokacin da suke yaki da ta’addanci da sauran barazanar tsaro. Ya ce tattaunawa ta sirri tsakanin majalisa da hukumomin tsaro za ta fi amfani a halin yanzu.
Rahotanni sun nuna cewa sanatoci 14 masu ci a yanzu sun sha kaye a zabukan fidda gwani na APC a jihohi daban-daban.
