Addu’o’in Ranar Dimukraɗiyya: Shettima ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya dawowar ɗaliban makarantu da aka sace cikin ƙoshin lafiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, ya ce Shugaba Bola Tinubu na cigaba da aiki tuƙuru domin tabbatar da ceto ɗaliban da aka sace tare da dawo da zaman lafiya da tsaro a sassan Nijeriya.

Shettima ya bayyana haka ne jim-kaɗan bayan kammala sallar Juma’a a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja a wani ɓangare na ƙarrama Ranar Dimukraɗiyya, yana mai jaddada matakin gwamnatin na shawo kan matsalar taɓarɓarewar tsaro.

Ya ce, gwamnatin Tinubu ta himmatu wajen magance matsalolin rashin tsaro da suka addabi wasu yankuna, inda ya jaddada cewa ana ɗaukar matakai masu ƙarfi ta hanyar haɗin-gwiwar hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a sassan ƙasar.

Ya kuma tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kubutar da waɗanda aka sace tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a fadin kasar.

A cewarsa, ƙoƙarin da ake yi na daga cikin ƙudirin gwamnatin Tinubu na tabbatar da tsaro da walwalar jama’a musamman a yankunan ke fama da matsalolin garkuwa da mutane da ta’addanci ga rayuka da dukiyoyin al’umma da kadarorin ƙasa.

By Babaji

Leave a Reply