Jigawa ta samu jarin Dala biliyan biyu daga kamfanin Chana

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana yarjejeniyar zuba jarin da ta ƙulla da wani kamfanin ƙasar Chana mai suna Hengtai Industrial Trading Company kan dala biliyan biyu a matsayin wani babban ci gaba da zai sauya fasalin tattalin arzikin jihar tare da ƙara buɗe sabbin damar kasuwanci da saka hannun jari.

Kwamishinan Muhalli na jihar ta Jigawa, Dakta Nura Ibrahim Kazaure, ne ya bayyana hakan a yayin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske kan sakamakon zaman Majalisar Zartarwar Jihar (SEC).

A cewarsa, majalisar ta samu rahoto kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin jihar ta rattaba hannu da kamfanin na ƙasar Chana, tare da nazartar ci gaban da aka samu tun bayan ƙulla yarjejeniyar.

Dakta Kazaure ya bayyana cewa, ƙarƙashin yarjejeniyar, kamfanin na Hengtai ya amince da zuba jarin dala biliyan biyu a Yankin Kasuwanci da Fitar da Kayayyaki na Musamman na Maigatari (Maigatari Eɗport Free Zone), inda za a gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban domin ƙarfafa samarwa da fitar da kayayyaki da ayyuka zuwa kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.

Ya ce, gwamnatin jihar ta ƙuduri aniyar samar da dukkan yanayin da ya dace domin samun nasarar aikin, tare da cika dukkan nauyin da ya rataya a wuyanta kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

“Wannan na daga cikin manyan jarin da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta samu nasarar jawo wa jihar. Da zarar aikin ya fara aiki yadda ya kamata, zai samar da ɗimbin guraben ayyukan yi tare da bunƙasa tattalin arzikin Jigawa da Nijeriya baki ɗaya, har ma da nahiyar Afirka,” inji Kwamishinan.

Har ila yau, ya bayyana cewa Majalisar Zartarwar Jihar ta amince da fitar da naira miliyan 517.7 a matsayin gudunmawar gwamnati ga mataki na biyu na Shirin Haɗin Gwiwar Horar da Ma’aikatan Noma Tsakanin Jigawa da China.

A ƙarƙashin wannan shiri, ɗalibai 50 masu karatun digiri na biyu (Masters) da kuma ɗalibai 15 masu karatun digirin digirgir (PhD) daga Jihar Jigawa na ci gaba da samun horo da ilimi a ƙasar Chana.

Dakta Kazaure ya sake jaddada ƙudurin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na ci gaba da maraba da masu zuba jari, gwamnatoci da sauran abokan hulɗa masu sha’awar saka hannun jari a Jigawa, musamman a fannonin da jihar ke da ƙwarewa da damar samun gagarumar riba.

Ya ce, gwamnatin jihar na ganin cewa jawo sabbin jarin cikin gida da na ƙasashen waje na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage talauci da kuma bunƙasa tattalin arzikin al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply