Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun sace ɗalibai 15, ma’aikata 4, sun kashe ɗan sanda 1 da masu gadi 2 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tashin hankali ya ɓarke a Kwalejin Aikin Noma da Kiwon Lafiyar Dabbobi da ke Bakura a Jihar Zamfara, yayin da wasu gungun ‘yan bindiga suka kai hari makarantar, Inda suka sace ɗalibai 15, ma’aikata 4, suka kuma kashe jami’in ɗan sanda ɗaya haɗa da masu gadi biyu.

Mataimakin magatakardar kwalejin, Aliyu Atiku, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ta wayar tarho da safiyar yau Litinin.

A Atiku, ‘yan bindigar sun mamaye harabar makarantar da misalin ƙarfe 10 na daren jiya Lahadi kuma sun kwashe kimanin sa’a ɗaya da rabi suna cin karensu babu babbaka a makarantar.

Ya ce, ma’aikata biyu da ɗalibi ɗaya sun tsere daga hannun ɓarayin bayan da suka sace su, yayinda suka dawo makarantar da sanyin safiyar yau.

Ya ci gaba da cewa, “Yanzu da nake magana da ku, mun gano a hukumance cewa ‘yan bindigar sun sace ɗalibai 15 dukkansu maza, mata uku da mutum ɗaya wanda su ma ma’aikatanmu ne kuma sun kashe masu gadinmu biyu da ɗan sanda ɗaya.”

Daga nan ya buƙaci Gwamnatin Tarayya, sojoji da ‘yan sanda da aka tura jihar don yani da ‘yan ta’adda da su ƙara himma don magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar jihar da munanan ayyukan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda don samun zaman lafiya.