’Yar shekaru 102 ta Musulunta a ƙasar Rwanda

Spread the love

Wata mata mai shekara 104 a duniya ta karɓi Musulunci a lokacin ta na ‘yar shekara 102.

Rahoton ya bazu a kafafen sada zumunta wanda ya nuna dattijuwar bayan ta karɓi addinin Musulunci duk da shekarunta.

Wannan na cikin wata sanarwa da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya yaɗa a ranar Juma’a 2 ga watan Mayun 2025 a shafin Facebook.

Mun kawo muku labarin yadda wata mata mai suna Fatima ta Musulunta a Kaduna, inda Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya ba ta kalmar shahada.

Malamin ya karbi matashiyar ne yayin karatunsa da ya saba yi a masallaci da ke birnin Kaduna a Arewacin Nijeriya.

Malamin ya ja hankalinta kan bin tafarkin Musulunci da aikata ibada bisa Sunnah, tare da yin haƙuri idan ta hadu da marasa kyawawan halaye.

Sheikh Assadus Sunnah ya yi mata addu’a Allah ya tabbatar da ita kan tafarkin addini, tare da yi mata fatan alheri a sabon matakin rayuwarta.

Shafin ya ɗauko sakon ne daga Daga Malamanmu wanda ke ɗauke da yadda matar da karɓi Musulunci a Rwanda.

Wani mutum mai suna Adnan Rashid ya bayyana yadda dattijuwar ta karbi Musulunci duk da yawan shekarunta.

Mutumin wanda dattijuwar ta karɓi Musulunci a hannunsa ya wallafa faifan bidiyo a Facebook domin tabbatar da labarin.

Mutumin ya ce: “Assalamu Alaikum kowa, ina tare da ‘yar uwarmu dattijuwa, shekarunta 104, an haife ta 1940.

“Ina da katinta yanzu don tabbatar da hakan, ta karɓi Musulunci shekaru biyu da suka gabata tana da 102.”

Mutumin ya ƙara da cewa, duk da tsufanta, tana san muhimman abubuwan Musulunci kuma tana zuwa masallaci kowace rana.

Ya ƙara da cewa, tana zuwa sallah daga safe har yamma, saboda tsufa, tana yin salla da jama’a.

Jajircewarta wajen addini duk da shekarunta ya burge dubban mutane a intanet, mutane sun yaba da tawalinta da yadda take zaman lafiya cikin Musulunci.

ɗaukacin mutane sun yaba da jajircewarta wnada ke tunatar da cewa shiriya na iya zuwa a kowane lokaci cikin rayuwa.

By ukarofi