Yunƙurin Amurka da Birtaniya da Australiya na yin haɗin gwiwa kan jirgin ƙarƙashin ruwa mai Amfani da makamashin nukiliya ya ci tura

Daga CMG Hausa

Yayin da wakilin ƙasar Sin ya ambato yadda aka tattauna batun haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen Amurka da Birtaniya da Australiya kan jirgin ƙarƙashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya a yayin babban taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta ƙasa da ƙasa wato IAEA karo na 66, ya nuna cewa, an tabka muhawara mai zafi kan wasu muhimman fannoni.

A ƙarshe dai an ki amincewa da daftarin dokar da suka gabatar na neman halasta batun haɗin gwiwarsu kan jirgin ƙarƙashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya.

Wasu al’ummomin ƙasashen yammacin duniya sun sha ambaton yadda ake bin doka da odar ƙasa da ƙasa, inda aka mayar da ƙa’idoji a matsayin harsashi.

Amma abun da suka yi ya saba wa abin da suka furta.

Haɗin gwiwar da ke tsakanin Amurka da Birtaniya da Australiya kan jirgin ƙarƙashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, ta saba wa manyan yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa guda 3 a lokaci guda, wato yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya wato NPT, da yarjejeniyar ƙa’idojin hukumar IAEA, da kuma yarjejeniyar tabbatar da rashin kasancewar nukiliya a yankin kudancin tekun Pacific.

Salibi da haka ne a yayin babban taron IAEA karo na 66, sakamakon ƙoƙarin da ƙasar Sin da sauran ƙasashe mambobin hukumar suka yi, ya sa yunƙurin ƙasashen 3 ya ci tura, lamarin da ya nuna cewa, masu adalci a duniya sun samu nasara, kana ana mutunta da kiyaye ƙa’idoji da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa, sa’an nan, Amurka ta sake yin rashin nasara a yunkurinta na yin danniya.

Mai fassara: Tasallah Yuan