Daga JOHN D WADA a Lafia
Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Nasarawa ta gudanar da zaɓen fidda gwaninta na ‘yan takarar majalisar wakilai ta tarayya a ranar 16 ga Mayu na shekarar 2026 inda ta sanar da waɗanda suka lashe zaɓukan a cikin mazaɓu huɗu daga cikin biyar da ke jihar.
Musa Shuaibu Guri wanda ya jagoranci kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwanin ne ya sanar da sakamakon kamar haka:
Mazabar Karu/Keffi/Kokona:
Daniel Ogazi ya lashe da ƙuri’u 13,083. Ya doke Danladi Jatau wato shugaban majalisar dokokin Jihar wanda ya samu kuri’u 5,873.
Sauran sakamakon a cewar sa shine kamar haka: Joseph M. Kaura ya samu ƙuri’u 1,429. Mohamed Nuraini Abdullahi Adamu, dan tsohon shugaban APC na ƙasa Abdullahi Adamu ya samu ƙuri’u 769. Mohamed Yakubu Dikko ya samu kuri’u 316.
Mazaɓar Nasarawa/Toto:
Mohammed Al-Bashir Babae Yarima ya lashe da ƙuri’u 31,796.
Ya doke ɗan majalisar da yayi wa’adi biyu wato Ari Abdulmumin Muhammad wanda yayi aiki daga 2015 zuwa 2023. Muhammad ya samu kuri’u 9,039.
Abdullahi Jibril Alassi ya samu ƙuri’u 3,728. Dr. Ahmed Wadah Ikaka kuma ya samu ƙuri’u 1,888.
Mazabar Akwanga/Wamba/Nasarawa Eggon:
Tony Bala Shammah ya lashe da ƙuri’u 38,333.
Dan majalisar tarayyar da yayi wa’adi ɗaya Hon. Jeremia Umaru wanda yayi aiki daga 2019 zuwa 2023, ya zo na biyu da ƙuri’u 4,061.
Mazabar Lafia/Obi:
Mohammed Ahmed Al-Makura ya lashe da kuri’u 45,000.
An dawo da shi ba tare da hamayya ba bayan Isaac Ali Kigbu ya janye. Al-Makura ɗan uwan tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne wato Umaru Tanko Al-Makura.
Mazabar Awe/Doma/Keana:
Zaɓen fidda gwani bai gudana ba a ranar Asabar a cewar shugaban kwamitin zaɓen.
Kwamitin yace har lokacin da ake tattara wannan labari zaɓen na cigaba da gudana a shiyar.
