Za a kammala gadar da Sin ke ginawa a Habasha a farkon badi

Daga CMG HAUSA

Kamfanin gine-gine na CCCC (China Communications Construction Company) na ƙasar Sin, ya ce za a kammala ginin gadar kogin Abay ta Habasha, mai tsawon mita 380, zuwa rubu’in farko na shekarar 2023.

Chen Li, manaja mai kula da aikin ginin gadar kogin Abay, ya ce ana sa ran za a kammala ginin wanda yanzu haka ya kai kaso 60, kafin rubu’in farko na baɗi.

Kafar yada labarai ta ƙasar Habasha FBC, ta ruwaito Chen Li na cewa, gadar zata tanadi hanya mai fadi ga masu tafiyar kafa, baya ga ababen hawa.

A nasa ɓangaren, Gebeyawe Belay, mataimakin janar manajan kamfanin gine ginen raya biranen Bahir Dar reshen jihar Amhara, ya ce bayan an kammala, fadin gadar zai kai mita 52.2, lamarin dake da nufin sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa a birnin.

Kamfanin CCCC ya shafe shekaru 20 yana aiki a Habasha, inda ya aiwatar da muhimman gine-gine ciki har da babbar hanyar Addis Ababa zuwa Adama mai tsawon kilomita 85 da babban zauren fasinjoji na babban filin jirgin saman Bole na Addis Ababa.

Ya kuma gina tare da kaddamar da yankunan raya masana’atun da dama, ciki har da na Mekelle da Jimma.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha