Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Babbar jam’iyyar hamayya a Nijeriya, PDP ta ce za ta ɗauki tsattsauran mataki kan mambobinta da ke ƙoƙarin shiga sabuwar haɗakar ƙawancen jam’iyyun hamayya ta ADC.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin amintattun jam’iyyar, shugaban jam’iyyar na ƙasa Ambasada Iliya Damagum ya ce jam’iyyar tana gargaɗi ’yan’yanta da ke shirin shiga sabuwar haɗakar ADC.

Damagum ya ce ƙoƙarin da haɗakar ke shirin yi ba zai yi tasiri ba, yana mai cewa da dama daga cikin mambobin haɗakar za su koma jam’iyyunsu.

“Yana da kyau su sani cewa babu inda ya kamata a haɗu domin tunkarar gwamnatin APC da ya wuce jam’iyyar PDP, amma in suna ganin ba haka ba, to su je su gwada su gani, amma dai na san dole za su dawo,” inji shi.

Shugaban riƙon ya kuma gargaɗi ’yan PDP da ya ce suna ƙoƙarin “sayar da jam’iyyar”.

Kawo yanzu dai akwai jiga-jigan PDP cikin sabuwar haɗakar ta ADC, ciki har da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar.

A farkon makon nan ne dai jam’iyyar PDP ta gudanar da taronta na Kwamitin Zartaswa da a ciki ta ce ta ɗinke ɓarakar da ta ɗauki tsawon lokacin tana fama da ita a cikin jam’iyyar.

By ukarofi