Za mu ci gaba da kare mutuncin ƙungiyar ’yan gwangwan a Nijeriya — Salisu Lale

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Babban Sakataren ƙungiyar ’Yan Gwangwan na Gidan Kwali, Ojota, Legas, Alhaji Salisu Lale, ya tabbatar da cewa shugabannin ƙungiyar za su ci gaba da ƙoƙarin kare martaba da mutuncin ƙungiyar a Legas da ma Nijeriya baki ɗaya.

Alhaji Salisu Lale, wanda asalinsa daga Jihar Kano ne amma yake zama a unguwar Gidan Kwali, Ojota, ya bayyana haka ne a Legas yayin taron bikin ƙaddamar da sabon shugabannin ƙungiyar na yankin ƙaramar hukumar Alimosho.

Ya ce, sabbin shugabannin da aka naɗa za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ci gaban ƙungiyar da kare martabarta a yankin Alimosho da ma Legas gaba ɗaya.

Sakataren ya taya sabbin shugabannin murna tare da yi musu fatan alheri, yana mai cewa, “Muna fatan zaku yi iyakar ƙoƙarinku wajen bunƙasa harkokin ƙungiyar da kuma kawo ƙarin cigaba kamar yadda sauran shugabanninmu a sauran ƙananan hukumomi ke yi.”

Ya kuma yabawa shugaban ƙungiyar na riƙon kwarya na kasa, Alhaji Ibrahim Abdullahi (Dan Soja), bisa jajircewarsa da sadaukar da kai wajen ganin ƙungiyar ta samu mutunci da ƙarfi a faɗin ƙasar.

Alhaji Lale ya jaddada cewa Dan Soja ya bayar da gagarumar gudunmawa, musamman ganin yadda ƙungiyar ke samun nasarori a jihohin Kudu da arewacin yammacin Nijeriya.

Haka kuma ya yi kira ga dukkan membobin ƙungiyar su ci gaba da zaman lafiya, su girmama juna, su zauna lafiya da sauran ƙabilu da suke mu’amala da su a Legas da ma sauran sassan ƙasar.

Ya ƙara da shawartar membobin ƙungiyar su riƙa bin dokokin gwamnati lokacin gudanar da harkokinsu, domin tabbatar da kyakkyawar mu’amala da hukumomin Legas.

Sai dai ya nuna damuwa kan yadda ma’aikatan jihar Legas ke matsa wa matasan su gudanar da sana’ar su ta gwa-gwan — ciki har da kamawa, korar su daga wuraren aiki, da takurawa hanyoyin da suke samun abincinsu.

Ya yi kira ga gwamnatin Jihar Legas ta duba wannan matsala domin nemo wa ’yan ƙungiyar madaidaicin mafita.

By ukarofi