Kungiyar Alƙalan Nijeriya ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Kungiyar Alkalai ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa Mal, Umar Namadi da lambar yabo a matsayan uban ƙungiyar na kasa, saboda ƙoƙarinsa nayiwa Addinin Allah shidima da gyara albashin Alkalai .

Kungiyar Alkalan ta kasa wadda Alkali Mudassir Hassan yake jagoranta tace sunzo gidan gwamnatine domin su jaddada goyan bayansu ga malam Umar Namadi Kuma su bashi lambar girma mawa saboda shidimar dayake yiwa musulunci da Kuma irin cigaban daya kawo abangaran sharia a jihar Jigawa.

Ya nuna gamsuwarsa da salon mulki irin na Gwamnatin malam Umar Namadi dubada irin gudun mawar da gwamnatinsa take baiwa Alkalai 

Yakuma godewa Gwamnatin jihar Jigawa akan irin goyan bayan da yakebaiwa Alkalai wajan basu horo su sami kwarewa akan aiki.

Abangare gida yakuma buƙaci Gwamnatin na madi daya taimakawa kungiyar wajan sayamasu motar hawa domin aiyukan da suka shafi ƙungiyar tareda gyara masu sakatariyarsu datake bukatar gyara domin su sami damar gudanar da ayyukan da suka shafi ƙungiyar.

Ya kuma buƙaci sauran Gwamnonin ƙasarnan dasuyi koyi da halaye irinna gwamnan jihar Jigawa wajan yiwa Addinin da sharia gata 

ɗaya daga cikin kwamashinonin jihar Alh Auwal Sankara ya baiwa kungiyar malaman Naira miliyan biyu a matsayan gudun mawarsa GA kungiyar Alkalan ta kasa

Da yake mayarda jawabi Gwamnatin Umar namadi ya yi alƙawalin gyara ofishin kungiyar Alkalan Kuma batun motar da da su yi anfani da ita, ita ce gwamnatin za ta duba buƙatunsu.

By ukarofi