Za mu ci gaba da yi wa ’yan ta’adda ruwan wuta — Babban Hafsan Sojojin Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar-Janar Faruq Yahaya ya ce dakarunsa sun shirya tsaf don kawar da dukkanin ‘yan ta’adda da maƙiya ƙasar nan daga doron ƙasa.

Janar Yahaya ya bayyana haka ne a ziyarar bikin ‘Easter’ da ya kai wa dakarun a barikin sojojoji na Maimalari da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

A jawabinsa, wanda kwamandan rundunar a yankin Arewa maso Gabas, Manjo-Janar IS Ali ya karanta, ya yaba da rawar da dakarun ke takawa wajen murƙushe ’yan ta’adda tare da wargaza maɓoyarsu a duk yankin da ma Yankin Tafkin Chadi.

Babban Hafsan ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa irin goyon bayan da yake bai wa dakarun ƙasar nan a fafutukarsu ta kawar da ’yan ta’adda a yankin da ma faɗin ƙasar nan.

Wasu daga cikin mahalarta bikin sun haɗa da dakarun rundunar OPHK da sojojin da suka samu raunuka a filin daga waɗanda yanzu suke murmurewa da sauransu.

Kazalika, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatan Jihar Borno, Barista Malam Fannami, yayin da Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Dokta Abubakar Ibn Umar Garbai Al’amin El-Kanemi ya samu wakilcin Zanna Wawurma na Masarautar Borno, Alhaji Usman Chiroma da sauran manyan baƙi.