Ɗangote ya ƙara wa Nijeriya matsayi da ƙima a duniya – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya yaba wa fitaccen ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Aliko Ɗangote, yayin da yake murnar cika shekaru 66 da haihuwa, tare da yi masa fatan Allah ya ƙaro tsawon rai, lafiya da kuma shekaru masu albarka.

Shugaba Buhari ya yaba masa bisa ɗimbin ƙoƙarin da yake yi domin ci gaban ƙasa.

Shugaban ƙasar a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu ya fitar, an ruwaito cewa, “Ina taya fitaccen ɗan kasuwa Aliko Ɗangote murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

“Ya ƙara wa Nijeriya daraja da ƙima a duniya. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba shi ƙarfi da hikimar da zai ƙara yi wa al’umma hidima.”