Za mu haɗu a kotu domin tabbatar da gaskiya – lauyoyin Natasha ga Gwamnati

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Lauyoyin Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan sun tabbatar da samun bayanan ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar akanta bisa rikicin rikicinta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, inda suka ce za su gabatar da hujjojinsu a lokacin da ya dace.

A sanarwar da Dakta Ehiogie West – Idahosa, SAN ya fitar a ranar Asabar, lauyoyin kuma sun nemi al’umma da su sanya su acikin addu’o’insu gami da na su goyon baya.

Ya ce, tawagar alķalan waɗanda suke karewa za ta shirya dukkan wata hujja da ake buƙata domin kare ababen da ake tuhumar wadda suke bai wa kariya kafin ranar shari’ar.

A ranar 16 ga watan Mayu, 2025 ne Gwamnatin Tarayya ta shigar da ƙarar Natasha bisa kalaman ɓatanci a wata hirar kai-tsaye a gidan telebijin, wanda ta ce ya saɓa wa dokar majalisa sashe na 391 da na kundin dokar ƙasa sashe na 89 na 1990.

Gwamnatin ta kuma ce, sanatar tana sane da cewa yin hakan zai zubar da mutuncin wanda ta yi kalaman akansa, saboda haka ta zayyano laifuka uku da take neman kotu ta yi hukunci akansu.

By Babaji