Da Ɗumi-Ɗumi: JAMB ta fitar da sakamakon ɗaliban da suka sake rubuta jarrabawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Haɗaka ta bada Gurbin Karatu ga Ɗalibai (JAMB) ta fitar da sakamakon jarrabawa ga ďaliban da suka sake rubutawa bayan tsaikon da aka samu a karon farko.

A wata sanarwa daga jami’in hulďa da jama’arta, Fabian Benjamin, ranar Lahadi, hukumar ta kuma bankaɗo wasu ayyukan satar jarrabawar daga ďalibai da wasu cibiyoyin jarrabawa.

Ya kuma ce, daga cikin ďalibai 336,845 da aka sake shirya musu jarrabawar, guda 21,082 ba su je rubutawa ba.

A watan da ya gabata ne aka rubuta jarrabawar ta zangon 2025, inda aka samu tsaiko daga ɓangaren sadarwa musamman a yankin Legas da wasu Jihohin Kudu masu Gabas.

Lamarin da ya sa JAMB ta shirya sabon jarrabawa ga waɗanda matsalar ta shafa a ƙoƙarinta na tabbatar da yin adalci a gare su.

By Babaji