Tinubu ya bai wa Nnamani, Anyim, Shema, Barkiya da wasu 18 muƙamai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ƙoƙarinsa na ƙarfafawa da inganta ayyuka, Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗa mutane 22 a wasu manyan muƙamai a Hukumomin Tarayya.

Daga cikinsu akwai sanannun jiga-jigan ƴan Jam’iyyar APC da suka haɗa da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamani; tsohon Sakataren gwamnati (SGF), Anyim Pius Anyim da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema.

An naɗa Nnamani ne a matsayin Shugaban Cibiyar Nazarin Tsare-tsare ta Ƙasa (NIPSS), yayin da aka naɗa Shema a matsayin Shugaban Hukumar Ci-gaban Birni, FCDA.

Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu kuwa, zai riƙe Darakta-Janar na Cibiyar Harkokin Wasanni, sai Isa Aremu, wanda aka sake naɗawa Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Ƙwadago ta Michael Imoudu, kamar yadda Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya wallafaa shafinsa na X.

Kakakin Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, an naɗa Yazid Shehu Umar Ɗanfulani a muƙamin Darakta-Manaja, Sanata Kabir Abdullahi Barkiya a matsayin Shugaban Hukumar Ci-gaban Filayen Noma ta Ƙasa, NALDA.

Sauran sun haɗa da Dakta Asabe Vilita Bashir – Darakta-Janar ta Cibiyar Ci-gaban Mata; Omobolanle Akinyemi Obe, Darakta-Janar na Cibiyar Harkokin Manyan Ƴan Ƙasa da Dakta Segun Aina a muƙamin Babban Jami’in Gudanarwa na Kwalejin Nijeriya.

By Babaji