Za mu yi wa sojoji 16 shari’a kan yunƙurin juyin mulki a Nijeriya – Rundunar tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rundunar tsaron Nijeriya ta ce ta kammala binciken da take yi kan yunƙurin kifar da gwamnati a Nijeriya wanda aka yi a shekarar da ta gabata, inda ta ce nan gaba kaɗan za ta gabatar da sojoji a gaban kotun sojoji domin fuskantar shari’a.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, wanda wannan ne karo na farko da ta fito ta tabbatar da an yi yunƙurin juyin mulkin.

A cikin sanarwar, wadda mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar, ya ce tuni rundunar tsaron ta miƙa rahoton bincike zuwa ga shugaban ƙasa.

“Rundunar tsaron Nijeriya na sanar da al’umma cewa an kammala binciken yunƙurin juyin mulkin da aka yi. Mun samu hafsoshi guda 16 da aikata laifuka da suka saɓa da tsare-tsaren aikin soji, kuma mun miƙa rahotonmu zuwa ga mataki na gaba kamar yadda doka ta tanada,” inji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa binciken ya gano tare da tabbatar da cewa wasu sojoji sun yi yunƙurin kifar da gwamnati, “sannan da sannu waɗanda aka gano sun aikata laifi za su bayyana a gaban kotun soji ta musamman domin fuskantar shari’a kamar yadda kundin tsarin soji ya tanada.”

By ukarofi