Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu ya sanar cewa nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara aiwatar da dokar hana kashe kuɗi fiye da ƙima a harkokin aure a jihar.
Da yake buɗe Masallacin Zawiyya Sheikh Aliyu Bunza da makarantar Islamiyya a Sakkwato, gwamnan ya ce, “Nan ba da dadewa ba za mu zauna da masu ruwa da tsaki a jiha domin sake duba dokar hana kashe kuɗi fiye da ƙima ga harkokin aure a jiha.”
Ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama wajibi ne ganin yadda masu shirin aure suke shan wahala a harkoki kafin ɗaurin aure, lamarin da ya ce ya ƙara sanya aure, ya yi wahala a tsakanin matasa mata da maza da suka kai lokacin yin aure.
A cewarsa kashe kuɗi fiye da kima almubazaranci ne da ke ba da gudunmuwa sosai wajen yawaitar tuzurai mata da maza.
Ya ce yawancin iyaye da magabata suna karya dokar takaita kashe kuɗin aure a jihar, inda suke yin almubazaranci a abubuwan da ba dole ba a yayin bukukuwan aure.
A cewarsa, saɓa dokar ya sa dole gwamnati ta shigo don tabbatar da abin doka yadda ya kamata.
Gwamnan ya ce albuzarancin ya taimaka wajen yawaitar halin rashin tarbiya a tsakanin matasa da suka kasa yin aure saboda tsadarsa ga abubuwan buƙata da ake nema.
Gwamnan ya yi kira ga iyaye da magabata da malaman addini da sarakunan gargajiya su goyi bayan gwamnati a tabbatar da dokar ta yi aiki.
A watan Mayun shekarar 2023 ne Majalisar Dokokin Jihar Sakkawto ta amince da dokar hana almubazaranci a harkokin aure.
Kudurin dokar, ɗan majalisa Abubakar shehu Yabo da Faruku Mustafa Balle suka samar, ta hana almubazaranci a bikin aure, zanen suna da sauran bukukuwan al’ada.
Sama da shekara biyu da samar da dokar amma ba a aiwatar da ita a harkokin aure a jihar.
