Zaɓen Anambara: Ba lallai a rantsar da Soludo a matsayin gwamna ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bincike a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Nijeriya, inda aka gudanar da zaɓe kwanan nan, kuma tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya zama wanda ya lashe zaɓen, ya bankaɗo wani babban batu, wanda fitaccen masanin tattalin arziki kuma ma’aikacin banki ya aikata.

Wani bincike ya nuna cewa, ɗan takarar jam’iyyar PDP, Valentine Ozigbo wanda ya zo na biyu a zaɓen gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga Nuwamba, 2021, ana iya rantsar da shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Anambra na gaba.

Ta kuma bayyana cewa, Farfesa Charles Soludo, na jam’iyyar APGA wanda ya fito a matsayin ainihin wanda ya lashe zaɓen da ake zargin ya shigar da ƙara ne a zaɓen gwamnan jihar Anambara 2021 a fom ɗinsa na EC9 wanda ya miƙa wa INEC.

Masu lura da harkokin siyasa sun bayyana hakan a matsayin babban kuskure.

Sai dai masana da masu ruwa da tsaki sun zaɓi bai wa kotunan shari’a damar yanke hukunci yayin da aka fara zaman sauraren ƙarar tare da bayyana fargabar sake yanke hukuncin shari’a irin na jihar Bayelsa.

Hakan dai ya haifar da tashin gwauron zaɓi a sansanin jam’iyyar APGA tare da sanin shigowa da kuma illar wannan babban kuskure ga al’ummar jihar Anambara, waɗanda suka fito suka yi watsi da barazanar da ake yi wa rayuwarsu, suka zaɓi ɗan takarar da suke so, Charles Soludo.

Sai dai wasu na ƙara nuna ɓacin ransu a kan waɗanda suka gano hakan, suka kuma zaɓi zuwa kotu, suna masu bayyana hakan a matsayin wani ɗan ƙaramin kuskure da kotun za ta yi watsi da ita ta kyale mutane su samu hanyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *