Tubabbun ‘yan Boko Haram sun yi zanga-zanga kan rashin cin nama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗaruruwan ‘yan Boko Haram da ke a sansanin da aka killace su bayan da suka miƙa wuya ga sojojin Nijeriya sun tayar da tarzoma a ranar Laraba da nufin gwamnatin ta dinga yanka musu shanun da ake kawo musu.

Tarzoma ta tayar da hankalun mazauna garin Maiduguri da ke kusa da sansanin tubabbun mayaƙan na Boko Haram, inda mazauna garin suka ɗauko adduna, takobi da kuma gariyo suna barazarar kashe duk ɗan Boko Haram ɗin da ya yi yunƙurin barin sansanin, a cewar majiyar da ta shaida wa kafar AFP.

Lamarin ya nuna yadda hukumomi suke fama da tsoffin mayaƙan Boko Haram, da kuma yadda mutanen gari suke tsananin tsorata da su matuƙar suka fantsama cikin gari.

A watanni da suka gabata ne sojoji suka gabatar da ɗaruruwan mayaƙan Boko Haram da suka miƙa wuya tare da iyalansu, a wata alama ta samun nasara da kawo ƙarshen ta’addancin da ya qi ci ya ƙi cinyewa a Arewa maso gabashin jihar Barno, amma duk da haka yawancin mazauna yankin suna ganin tubabbun a matsayin babbar barazana ga barkar tsaro.

Aƙalla mayaƙan Boko Haram 250, tare da mata da ƙananan yara suka tayar da hatsaniya da zanga-zanga a Gidan Taki,  Boko Haram ɗin sun a karairaya tagogi da ƙofofi da yin barazanar ficewa daga sansanin matuƙar ba a biya musu buƙatun su ba, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida.

“Tubabbun ‘yan Boko Haram sun tada hayaniya da safen nan, sun karairaya ƙofofi da tagogi, har ma da ƙoƙarin guduwa daga sansanin,” inji Konto Garga mai yaƙi da da’awar ‘yan Boko Haram, kuma wanda ke taimakon sojoji.

A cewar rundunar sojin Nijeriya, mayaƙan Boko Haram 18,000 tare da iyalansu ne suka miƙa wuya ga sojoji bayan mutuwar babban kwamandan ƙungiyar, Abubakar Shekau cikin watan Mayu, 2021.

Shekau ya halala kansa ne domin guje wa kamawa yayin da suka samu saɓani da ƙungiyar ISWAP a dajin Sambisa.

ISWAP ta ƙulla ƙawance da Boko Haram a shekarar 2016, inda suka samu mazauni a Nijeriya da nufin yin jihadi.

Da yawan mazauna garin Maiduguri sun nuna fargabar su da tuban mayaƙan Boko Haram ɗin, inda suke ganin da yawan mayaƙan za su iya fantsama cikin gari su haifar da gagarumar matsala ga tsaro a yankin.
 
Masu zanga-zangar da ke zaune a sansanin tun watan Agusta, sun buƙaci hukumomi su miƙa musu shanun da ake kawo musu kullum domin yanka musu, a maimakon a dinga kawo musu yanka-yanka daga kwata, kamar yadda majiyar ta ambata.
“Mutanen da ke zaune a yankin sun fito da makamai za su kashe duk wani wanda ya fita daga sansanin,” inji Garga.

“Har yanzu mutane suna kallon su a matsayin barazana ga tsaro,” inji Garga wanda ɗaya ne daga cikin jami’an tsaro na musamman.

Wani mazaunin Gidan Taki mai suna Usman, ya ce mutanen yankin ba su yi amanna da sahihancin tubar ‘yan ƙungiyar ba, inda sannan zanga-zangar ta tabbar musu da hakan, inji shi.

“Idan har suka fita daga sansanin ba za mu lamunta ba, dole mu san yadda muka mayar da su saboda mun san haɗarin da ke tattare da su,” cewar Usman.

“Ƙoƙarin da mutanen gari da jami’an tsaro suka yi a kai shi ya taƙaita tarzomar har tsararrun suka koma gidajen su,” inji Bunu.

Tarzomar dai ita ce ta biyu a sansanin, tun bayan wadda suka yi a watan Disamba akan irin wannan buƙatu, kamar yadda wani jami’in tsaro Babakura Kolo ya bayyana.

Tubabbun ‘yan Boko Haram ɗin sun sha yin gardama da kace-nace da waɗanda ke tsaron su a sansanin da su ke killace.

“Har yanzu Boko Haram su na da wannan haukan nasu, kuma suna cin mutuncin mutanen mu  a matsayin su na wakilan gwamnati,” inji Kolo.