Tattalin arziki da tsaro: Nijeriya ta samu tagomashi da koma-baya

*Hauhawar farashi zai jefa ’yan Nijeriya miliyan shida cikin talauci – Bankin duniya

*Fyaɗe 11,200 aka yi a Nijeriya daga bara zuwa bana – Amnesty International

*Tattalin arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.03 a 2021 – NBS

*Yanzu babu tursasawar addini a Nijeriya – Amurka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Daga dukkan alamu al’amuran Nijeriya su na yin kwangaba-kwanbaya ko kuma a ce tafiyar kura, inda yayin da a wani fannin ta samu cigaba, a wani fannin kuma ci-baya ta samu. Ga yadda Manhaja ta haɗo muku rahotanni kan halin da ƙasar ke ciki, musamman ma a wannan mako:-

Bankin Duniya:
Bankin Duniya ya gargaɗi gwamnatin Nijeriya cewa, ’yan Nijeriya miliyan shida na iya tsunduma cikin baƙin talauci sakamakon hauhawar farashin kayan abinci.

Bankin wanda ke zamansa a Amurka ya shawarci gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin gaggawa.

A watan Yuni, bankin ya ce, a 2020, aqalla ’yan Nijeriya miliyan bakwai ne suka faɗa cikin talauci sakamakon hauhawar farashin abinci kaɗai.

Bankin ya yi amfani da binciken ‘National Longitudinal Phone Survey’ (NLPS) wajen ganin illar cutar Korona kan rayukan mutane da jin daɗin iyalai.
Binciken NLPS wani haɗin kai ne da ke gudana tsakanin hukumar lissafin Nijeriya NBS da na bankin duniya.

A cewar rahoton bankin, “hauhawar farashin kayan masarufi tsakanin Yunin 2020 da Yunin 2021 na iya jefa wasu mutum miliyan shida cikin talauci, musamman waɗanda ke birane.

“Wannan bincike ya nuna cewa masu fama da baqin talauci a Nijeriya sun ƙaru daga kashi 40.1 zuwa 42.8 sakamakon hauhawar farashin abinci tsakanin Yunin 2020 da Yunin 2021,” inji rahoton.

Hakan na nufin cewa ƙarin ’yan Nijeriya miliyan 5.6 za su sake dilmiya cikin talauci. Yanzu talauci ns daf da zama ruwan dare a Nijeriya.

Ƙasar Amurka:
Ƙasar Amurka ta cire Nijeriya daga cikin jerin ƙasashe masu keta haddin addini ta fuskar tursasawa, kamar yadda ta sanya Rasha, Chana da kuma wasu ƙasashe takwas ba tare da izini ba, a matsayin ƙasashen da ba su damu da bayar da ’yancin addini ba.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba mai taken ‘’Yancin Addini’.

Yayin da ƙasar Amurka a shekarar 2020 ta sanya Nijeriya da wasu ƙasashe shida cikin jerin ƙasashe musamman da suka shiga ko kuma suka amince da cin zarafin addini, Nijeriya ta fita daga jerin ƙasashen da aka sanya a cikin 2021 na cin zarafin addini.

Blinken, wanda a halin yanzu yana ƙasar Kenya ta Gabashin Afirka domin ziyarar aiki, an kuma shirya kai ziyara Nijeriya a cikin wannan mako inda za a gana da shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, da sauran mambobin majalisarsa.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, a cikin sanarwar da ya bayar a ranar Laraba, ya ce, “amurka ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen bayar da ’yancin yin addini ko ga kowa da kowa a kowace ƙasa. A wurare da yawa a duniya, muna ci gaba da ganin gwamnatoci suna tursasawa, kamawa, yi wa mutane barazana, ɗaure su, da kuma kashe mutane kawai don neman su yi rayuwarsu daidai da imaninsu.

Wannan Gwamnatin ta himmatu wajen tallafa wa ’yancin kowane mutum na ’yancin yin addini, gami da fuskantar da yaƙi da masu take haƙƙin ɗan adam.

“Kowace shekara Sakatariyar Harkokin Wajen ta na da alhakin tantance gwamnatoci waɗanda, saboda tauye ’yancinsu na addini, sun cancanci a sanya su a cusa su cikin ƙarƙashin dokar ’yancin addini ta duniya. Ina sanya Burma, Jamhuriyar Jama’ar Sin (Chana), Eritriya, DPRK, Pakistan, Rasha, Saudi Arabia, Tajikistan, da Turkmenistan a matsayin ƙasashen da suke take haƙƙin musamman saboda shiga ko jure wa tsare-tsare, ci gaba, da kuma mummunan cin zarafi na ’yancin addini,” inji ta.

Ƙungiyar Amnesty:
Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana cewa, mata da ƙananan yara aƙalla 11,200 ne aka yi wa fyaɗe a Nijeriya a shekarar 2020.

Amnesty ta ba da wannnan alƙaluman ne a sabon rahotonta kan fyaɗe da cin zarafin mata da ƙananan yara.

Ƙungiyar ta fitar da duk wannan rahoton ne bayan binciken da ta gudanar tsakanin watan Maris na 2021 zuwa watan Agustan 2021 a kan ƙararrakin fyaɗe da cin zarafin mata da ƙananan yara, ciki har wata mai shekara shida da mai shekara 11 da aka yi musu aika-aika.

Binciken ya gano cewa, rashin ɗaukar ƙwararan matakan magance matsalar fyaɗe da cin zarafin mata daga ɓangaren gwamnati ya sa matsalar ke ta ƙara ɗaruwa, domin masu aikata laifukan na ta ƙara tsaurin ido a Nijeriya.

Rahotan ya ce, “waɗanda aka yi wa fyaɗe ba sa samun adalci, ba a gurfanar da waɗanda ake zargi, akwai kuma ɗaruruwan laifukan fyaɗe da ba a bayar da rahotonsu ba saboda tsoron muzantawa ko ɗora laifin a kan waɗanda aka yi wa fyaɗen, sannan akwai batun rashawa da shi ma ke hana ɗaukar mataki, wanda duk dai sakamakon rashin ɗaukar tsuraran matakai ne don magance matsalar yadda ya kamata ba a Nijeriya.”

A shekarar da ta gabata, Nijeriya ta yi fama da tashe-tashen hankula a yanar gizo da zanga-zangar tituna bayan da aka yi ta fama da kashe-kashe da fyaɗe da ake yi wa mata.

’Yan sanda sun ce a cikin watan Yunin 2020 cewa, ƙasar ta sami ƙaruwar fyaɗe da cin zarafin mata a gida yayin kullen Korona.

Ministar harkokin mata, Pauline Tallen ta kuma ce, adadin cin zarafin mata da ƙananan yara ya ruvanya sau uku yayin da waɗanda abin ya shafa ke maƙale a gida.

Gwamnonin jihohin dai sun sanar da kafa dokar ta-ɓaci kan lamarin, inda suka ce, sun himmatu wajen tabbatar da cewa masu laifin sun fuskanci hukunci.

Sai dai Amnesty ta ce, Nijeriya na kokawa da ra’ayoyin al’adu, gazawar jami’an tsaro wajen gudanar da bincike, da kuma rashin tallafa wa waɗanda suka kuɓuta.

Daraktan Amnesty International a Nijerriya, Osai Ojigho, ta bayyana cewa, tsoron a ɗora wa matan da aka yi wa fyaɗe laifin abin da ya same su ko ƙaryata su ya hana yawancinsu kai ƙara, ballanta maganar neman samun adalci.

Ta ce, “duk da cewa hukumomin Nijeriya sun ayyana dokar ta ɓaci a kan cin zarafin mata da aikata fyaɗe, amma ana ci gaba da aikata laifukan a mataki mai tayar da hankali.”

Hukumar NBS:
Babban jami’in hukumar ƙididdiga ta tarayya, Simon Harry, da kuma shugaban ofishin ƙididdiga na ƙasa, ya bayyana cewa, tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru da kashi 4.03 cikin ɗari a cikin kwata na uku na 2021.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a wani taron manema labarai kan halin da ake ciki a halin yanzu na tattalim arziki.

Harry ya yi bayanin cewa, alƙaluman marasa kyau da aka rubuta su a cikin 2020 sakamakon cutar ta Korona suna da mummunar tasiri akan alƙaluman na yanzu na kwata biyu da uku 2021.

Ya bayyana cewa, ci gaban da aka samu a kashi huɗu na ƙarshe ya nuna ci gaban da aka samu wajen daƙile cutar ta Korona da kuma mummunan tasirin da ke tattare da rayuwa, jin daɗi da tattalin arziki.

Ya ce, “a duniya baki ɗaya, ƙasashe da yawa sun shaida ci gaba a ayyukan tattalin arziki idan aka kwatanta da 2020 lokacin da Korona ke yaɗuwa.

“Don haka, farfaɗo da tattalin arzikin wani tsari ne a hankali wanda ke buƙatar ci gaba da ƙoƙarin haɗin gwiwa don inganta ayyukan tattalin arziki a sassan hukumomin. Duk da haka, a Nijeriya, fatan samun cikakken murmurewa na ƙara fitowa fili idan har aka ci gaba da ɗorewar halin da ake ciki na inganta ayyukan tattalin arziki a sauran shekara da kuma bayan haka,” inji shi.

Yana da muhimmanci a ambaci cewa, ci gaban tattalin aiziki na shekara-shekara na 2021 ya tsaya a  1.92 bisa ɗari.

Bayanin na rahoton ya nuna cewa, jimillar GDP ya kai Naira tiriliyan 45.113 a wa’adi, wanda hakan ya fi girma idan aka kwatanta da kwata na uku na shekarar 2020, wanda ya samu jimillar GDP na Naira tiriliyan 39.089, wanda ke nuni da samun ci gaban shekara-shekara.

Dangane da ɓangaren mai kuwa, rahoton ya ce, al’ummar ƙasar, a kashi na uku na shekarar 2021, an samu matsakaicin yawan man da ake hako ganga miliyan 1.57 a kowace rana (mbpd).

Wannan, inji shi, ya yi ƙasa da matsakaicin adadin yau da kullum na 1.67 da aka rubuta a cikin kwata zaya na 2020 da 0.10 kuma ƙasa da kwata na biyu na 2021 ƙarar samar da 1.61 ta 0.05.

Har ila yau, ta ce, haƙiƙanin ci gaban da aka samu a fannin mai ya kai kashi 10.73 (shekara-shekara) a cikin kwata uku na shekarar 2021, wanda ke nuni da ƙaruwar da kashi 3.16 cikin 100 dangane da adadin da aka samu a kwata na shekarar 2020.

Ya ƙara da cewa, ɓangaren mai ya ba da gudummawar kashi 7.49 bisa jimillar GDP na hakika a cikin kwata, ya ragu daga alƙaluman da aka rubuta a daidai lokacin shekarar 2020 kuma sama da kwata na baya, inda ya bayar da kashi 8.73 bisa ɗari da kashi 7.42 bisa ɗari.

A ɓangaren da ba na man fetur ba, NBS ta ce, ya ƙaru da kashi 5.44 bisa 100 a cikin kwata-kwata, wanda ya haura da kashi 7.95 bisa ɗari idan aka kwatanta da adadin da aka samu a kwata guda na shekarar 2020 da kashi 1.30 cikin 100 idan aka kwatanta da kwata na biyu na 2021.

Ya ce, “sauran su ne noma (samar da amfanin gona) da kuma sufuri da adanawa,  wanda ke haifar da ingantaccen ci gaban tattalin arziki.

GDP yana taimaka wa wajen tantance tsari da yanayin tattalin arziki, wanda ta hanyar ma’ana yana auna ayyukan tattalin arziki a cikin wani lokaci da aka ba shi.