Yadda kyakkyawar zamantakewa ke kawo zaman lafiya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A wannan mako ina son hankalin mu ya karkata ne wajen nazarin yadda halayya ta gari da kyautatawa juna a mu’amala ta yau da kullum ke iya haifar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama’a, musammam mutane masu bambancin ƙabila, addini ko ra’ayin siyasa, da sauran harkoki da zaman tare ke iya haɗa jama’a, daga ɓangarori daban-daban.

Babu shakka zaman lafiya da jama’a, tausayawa, tallafawa, da kaucewa duk wani abu da zai iya kawo saɓani da rashin fahimta a tsakanin mutane, abin a yaba ne matuƙa, babu ma kamar wannan lokaci da jama’a ke cikin ƙunci da rashin yarda da juna, saboda kurakuran da suke zargin wasu suna yi da gangan, don cimma wata manufa ta son ran su, ko danne haƙƙin wasu.

Rashin yarda, zargin juna, hassada, kishi, zalunci, babakere, da tauye haƙƙin raunana, halaye ne da aka saba gani a zamantakewa ta yau da kullum, inda wasu ke ƙoƙarin fifita kansu da tilasta buƙatun su kan na sauran mutane, a dalilin haka kuma sai a samu turjiya da nuna rashin yarda daga wani ɓangare.

Ɗaya daga cikin halayen da ke zama ƙalubale ga cigaban zumunci da zamantakewa shi ne son kai. Mutane masu son kansu suna haifar da damuwa, qunci da ƙiyayya mai yawa, saboda sun fifita son zuciyarsu a kan amfanin da jama’a da dama za su samu. A kan abu ƙalilan da wani yake ƙwadayin samu sai ya rusa jin daɗin da ƙoƙarin da wasu suka daɗe yana yi.

Mun sha jin ƙorafe-ƙorafe daga mutanen da aka tauye wa haƙƙi ko aka zalunta, sakamakon son zuciyar da wani ya nuna musu, don kawai ya samu damar da zai yi abin da ya dace amma ya kasa, saboda zarmewa da son zuciya.

Akwai mutanen da za ka riƙa yi musu kallon manya ana girmama su saboda matsayin da suke da shi, ko arzikin da Allah ya ba su, har ma ka ji ana yi musu kirari, don kwaɗayin samun wata alfarma daga wajensu. Sai dai da a ce za ka samu jin abin da waɗanda ke ƙarƙashin sa ko iyalinsa suke faɗa, ba za ka so ka sake kallon sa da martaba ba. Saboda halinsa na rashin fitar da haƙƙin waɗanda suka yi masa ƙwadago da gumin su, sauke nauyin iyali da ‘yan uwa da ke kansa. Yana ganin idan ya cire wani abu daga arzikin sa to, zai rage masa jin daɗi, ko zai bayar a inda ba a san zafin su ba.

Ya na yi wa mutane wahala su sadaukar da wani ɗan yanki na jin daɗin su, walwala ko damar da suke da ita don wani ya amfana. Sai ka ga ana ta fama da wani a cikin motar haya kan ya ɗan gyara zamansa domin kowa ya ji daɗin zama, amma mirsisi sai ya qi, saboda tunanin idan kowa ya zauna da kyau shi ba zai sake yadda yake so ba. Haka ma ko a gaban ubangiji wajen sauke farali, za ka ga wani ya yi babakere a waje ana roƙon sa ya gyara zama ko tsayuwar cikin sahu, amma yana ganin za a takura masa shi ba zai yarda ba.

A duk yayin da mutane suka fahimci wane yana da halin rowa, son kai da rashin sassauci a harkokin rayuwar to, yana zama abin ƙyama da yi wa kaffa-kaffa. Kyautatawa da nuna halin kwarai suna sanya ƙaunar mutum a zuciyar abokan zamansa da sauran ‘yan uwa.

Sau da dama an sha samun asara mai yawa ta rai ko ta dukiya, da vacin rai mai tsanani, saboda wani ya kasa haƙuri a samu yadda ake so ko ya yi abin da ya kamata daga ɓangarensa, don yana ganin ba shi ne zai amfana ba, ko kuma idan ya yi haka zai takura.

Eh, ba an ce lallai mutum ya riqa takurawa kansa don jin daɗin wasu ba ne, amma kyautatawa tana da amfani, kuma akwai alheri da ke bin bayan sadaukarwa ta tsakani da Allah. Ba kowanne lokaci ne yin abin da ya kamata ke zama takura ba, sauke nauyi ne. Kai ma wani lokaci za ka nemi wani abu daga wajen wani, wanda ka ke ganin ya kamata ya yi maka, idan bai yi ba kai ma ba za ka ji daɗi ba.

Mutane masu son zuciya ba su taɓa samun wadata da gamsuwa da rayuwarsu ko da kuwa sun samu damar yin duk abin da su ke so, saboda ko da yaushe tunanin su ba ya wuce jin daɗin kansu ta hanyar ƙuntatawa wasu.
An rawaito a hadisi ma’aikin Allah mai tsira da aminci yana cewa, imanin ɗayanku ba zai cika ba, har sai ya so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa.

A nan za mu fahimci cewa, ashe kyautatawa don jin daɗin wani ko wasu addini ne, kuma alama ce ta cikar imani. Kyautatawa a yayin zamantakewa tana ƙara ƙauna, zaman lafiya, girmamawa, da mu’amala mai daɗi tsakanin mutane. Ba sai ka fito ka nuna kana son girma ko neman ɗaukaka ba, halinka nagari kaɗai ya isa ya saya maka duk wata daraja da ka ke nema.

Idan kuma ka na neman abin da nan da nan zai zubar maka da kima da rashin daraja a idon mutane har na ƙasa da kai to, ka danne haqqin wasu ko ka fifita son kan ka a kan na sauran jama’a. Ƙasƙanci da zubewar mutunci na zuwa ne inda son zuciya, haɗama, da danniya su ka yi katutu.

Don haka kirana ga ’yan uwa masu karatu shi ne a guji fifita son rai, domin an ce son zuciya bacin zuciya!