Wa ke da laifin lalacewar yaranmu mata?

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Assalamu Alaikum, kamar kullum, ga mu yau ma a cikin filin mu na tarbiyya. Za mu ɗauko batu mai matuƙar mahimmanci da amfani da ya kamata kowaɗanne iyaye su sa ido su kuma cire soyayya su ajiye gaskiya a kan yara. Ƙila wasu iyayen sun san me yaransu suke aikatawa a bayan idanunsu, ƙila kuma ba su sani ba. Ban gaskanta hakan na faruwa ba sai da na ji daga bakin yara matasa mata da maza kusan mutum shida sai abun ke ɗaure min kai, da gaske ne ko da wasa? Na ɗan bincika na tarar da zancen akwai shi. To sai dai mu ce innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Allah Ka raba mu da zamani, Ka kuma shirya mana yaranmu.

Makarantu ma fa na da alhakin su ringa nusar da yara irin taɓargazar da suka sa kansu. Don masu magana sun ce, ɗa fa na kowa ne, ba ka san inda naka za shi ba. To dole sai mun haɗa ƙarfi da ƙarfe, mun gyara yaranmu. Gaskiya abun ya fara ɓaci, ko ma na ce ya ɓaci. Kar mu shiga nasiha ta yi tsaho, mu shiga maganar da ta kawo wannan hannunka mai sanda da na yi.

Iyaye: Iyaye da suka bar yaransu mata na kwana a cikin makaranta ta jami’a anya sun san me yaransu wasu ke aikatawa bayan su sun bar su a matsayin karatu suke? Idan ba su sani ba, to su sani su kuma sa-ido. Idan ɗanka ko ‘yarka ba ta yi, to ka yi hamdala, amma ka sa mata takunkumi na nasiha don gudun kar kwaɓarta ta yi ruwa. Ka kai yarinya makaranta karatu, ba ka san fitina take ba. Idan dare ya yi ficewa suke hira ko a ɗebe su a mota a fita da su. Wasu a daren ake dawowa da su, wasu kuma sai gari ya waye. Ya ilahil alamina, yaushe duniya za ta zauna dai-dai? Kuma ba komai ke jawo haka ba, illah kwaɗayi da huɗubar shaiɗan da haɗuwa da mugayen ƙawaye ko abokai da suke tama’ali tsakaninsu. Wannan ba ƙaramar magana ce da za a ce, a yi shiru ba.

Dole laifin iyaye ne. Don me za ki saki ɗiyar da kika haifa? Za ki kai ta cikin makaranta ita ɗaya babu mai saka mata ido, wai da sunan karatu. Ban ƙi da wanda suke zuwa daga wasu garuruwan ba, amma kai naka na kusa da kai wanne kwana  za ta yi a makaranta?

Gabaɗaya yanzu duniyar ta rikice, babu mai gaskiya, babu nagari. Dole sai ka sa wa yaranka sabuwar ƙwaƙwalwar da za su ringa gina rayuwarsu, da yadda za su amfana da rayuwar su a gaba. Amma idan an lalata tun daga ƙuruciya, to fa ƙarshe nadama ne.

Salon da suke bi a yanzu: Salon da suke bi yanzu da wuya a gane sai  ana dubawa. Wai har cika bakinsu suke yi cewa, idan har kana da kyau ba ka sai da kyawun ba, ba ka cika ba. Ya Allahu wato tutiya suke da kyau sun manta shi kyawun ai amfaninsa kaɗan ne. Idan ya gushe, ko kallon ki ma ba su yi, mazan. In dan su kike yi, to za su kai ki, su baro ki a ruɗin duniya. Sannan da kanki ki zo kina kuka, su kuma su samu kintsattsiyar mace wacce ta fi ki kyau da komai su aura, ke kina cizon yatsa. Tarbiyyar da iyaye suka ba ki, kin rusa akan wani jin da]in duniya kaɗan, na lokaci kaɗan. Meye amfanin sa? Ba za mu hana yara karatu ba, amma yana da kyau a san me suke yi a karatun, yaya rayuwar su take.

Su kuma maza manya masu zuwa suna hure wa  yaran mutane kunne a makaranta suna ba su abun duniya, suna lalata musu rayuwa, su tuna su ma fa sun haifa kuma wallahi komai daren daɗewa, komai tsaron da ka yi musu, kai ma fa sai an ma naka. Saboda faɗa ce ta Allah(SWT), da ma’aikin Allah, (Sallallahu alaihi Wasallam). Duk abunda ka shuka, sai ka girbe shi tun a duniya kafin ka je lahira. Yana da kyau mu san yara dai amana ne a gurinmu, Allah zai yi hisabi tsakaninmu da yaranmu. Don ALLAH mu farka, don Allah mu yi wa yaranmu tarbiyya tagari.

Duk da a gidan ma yaran binne iyaye suke da wayo a ganinsu sun fi iyayen wayo. Yarinya za ta shirya da sunan biki kuma sharholiya ta tafi. Wallahi kina zaune ba ki hayam, ba ki ma san me ɗiyarki take aikatawa ba. Uwa ta sa ido irin kayan da yaransu ke sawa, sun dace ko kuwa? Shi ma da uba yana da kyau ya taimaka wa matarsa wajen sa-ido a kan rayuwar yaransu.

Ba a ce uwa ce kawai mai ba da tarbiyya ba, shi ma har da shi. Don shi yana fita kuma ba zai taɓa cewa bai san me yara suke aikatawa a waje ba. Daga sutura za ka gane yaya rayuwar ɗanka take. Yanayin shigar kaya da yara ke yi, zai jawo hankalin iyaye su san idan ɗansu ya kauce hanya, tun kafin a yi nisa, a taka wa yaro birki. Amma idan za ki yi shiru, akwai damuwa. Wallahi mun shiga wani irin yanayi na kuka da tarbiyya wanda ba ma yara kaɗai ke buƙatar garawa ba, har manyan su ma da nasu salon rashin mutuncin da suke aikatawa. Wanada insha’Allah sati mai zuwa za mu duba nasu. 

Matasa daga shaye-shaye, sai ƙwacen waya, sai fitina, sai garkuwa da yara ƙanana ‘yan  shekara 19 zuwa sama, su ne suka rikita ƙasa abun mamaki. Sai ka ga yara masu ƙarancin shekaru, a zuga uban kuɗi a ba su, ka fanshi ɗanka. Mun shiga uku da zamanin da taɓarɓarewar rayuwa ta yi yawa. Kuma duk rashin tarbiyya da rashin ilimi, da rashin aikin yi ya jawo waɗannan abubuwan da suke ta faruwa kamar ana daɗa ƙara fetur. Allah ya farkar da mu, ya kawo mana ɗauki.

Uwa ba ta so a yi wa ɗanta faɗa, kawai don son rai. Uba ba ya sa ido a kan ɗansa kawai don bai damu da rayuwarsa ba ko gani yake ɗan nasa daban ne. Yara ba sa son a yi musu faɗa, yanzu sa ɗau gaba da ƙunci da mutum. Maƙoci ba ya shiga sabgar gidan maƙocinsa, gudun kar ya yi magana, a ci masa mutunci, ko kuma kawai shi bai ɗauki maƙocin nasa da daraja ba, ba ruwansa da duk abun da zai yi, shi ta shafa.

Malamai ba sa duba rayuwar yaransu da aka ba su amana. Duniya ba ta son gaskiya, kowa yadda ya ga dama yake yi. Wanda duk wannan ba koyarwa ce ta addini ba, lissafi ne kawai na mutum.

Matasa don Allah ku ji tsoron Allah, ku kyautata wa kanku rayuwa, ku tausaya wa iyaye dake faɗi-tashi don inganta muku rayuwa. Ita rayuwar ba ta da tabbas. Har gwara ɗa Namiji a kan mace. Ita ba ta da abun kariya. Idan ba ta kare kanta ba, to sai girma ya zo za ta yi ta cizon yatsa, tana da na sani. Saɓanin namiji shi komai ya yi ado ne.

Nadamarsa ba ta kai ta mace ba, da za ta gidan wani ta haifi yara. Idan ta sake mijin ta ya san me ta aikata, to duk mutuncinta sai ya zube a gurinsa. Kuma ba zai yadda da ita ba. Sai zama ya sake salo, haka za a yi ta tafiya. idan auren ma ƙwari ne. To amma idan ba mai ƙarko ne ba, sai ya koro ki ya auro tagari, kin ga kin yi biyu babu. Saboda haka, mu daure mu yi wa kai faɗa. Uwa tai ta nusar da ‘yarta muhimmancin kare kai. Ta tsorata ta da abun da yake faruwa. Idan an yi auren ta san darajar mutuncinta da budurcinta. Shi ne kariyar kowacce ɗiyar kirki. Idan kin kasa a titi kuma, to ƙarshenta babu daɗi.

Allah sa mu dace. Abunda muka yi na dai-dai, Allah ya yi masa albarka. Abun da muka yi na ba dai-dai ba, ALLAH Ya yafe mana.

Mu cigaba da karanta Jaridar Manhaja, irin ta daban ce. Wassalam.