Ko Gaddafi zai dawo Libya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Wani faifan bidiyo da editan jaridar Manhaja, Nasir S. Gwangwazo, ya saka a shafinsa na yanar gizo ya ja hankalina kan mulki da yadda ya ke da kuma yadda zai iya kasancewa idan ba a kai ba ko idan ya kuvuce. A cikin bidiyon, Kakakin tsohon Shugaban Nijeriya Jonathan, wato Reuben Abati, ke bayani kan kwanakin ƙarshe na mulkin maigidansa a 2015, inda ya zama mutane da a baya ke tururuwa zuwa fadar Aso Rock su ka yanke cak kamar an ɗauke ruwan sama.

Kafin lokacin Abati ya ce, mutane ke jerin gwanon neman ganin Jonathan ba masaka tsinke, amma yana shan kaye a zaɓe sai mutanen su ka koma gidan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado a lokacin, wato shugaba na yanzu, Muhammadu Buhari.

Gabanin na ga faifan bidiyon, na taɓa ganin wani rubutu da Abati ya yi, inda ya ke cewa, bayan rasa shugabanci, sai ya ɗauka ko wayarsa ta salula ta ɓaci ne, don wataƙila ya kai ta gyara, don tamkar an daina buga ma sa waya idan aka duba yadda a baya wayar tasa ba ta shiru daga masu neman bayanai kan shugaban, musamman ’yan jarida.

Haka nan ya duba da kyau ya tabbatar da lafiyar wayar ƙalau, kawai dai an daina buga ma sa ne, don ba a yayin labarin maigidansa a lokacin, an koma ga shugaba mai shigo wa mulki. Reuben Abati ya yanke hukuncin taron mutane a wajen mai mulki yayin da ya ke kan kujera ne, don da zarar ya sauka sai a watse a bar shi da halinsa.

A cikin bidiyon can, bai kammala bayanin ba sai da ya ce, hatta a filin jirgi bayan sun zo raka Jonathan, don koma wa garinsu na haihuwa, wato Otuoke a Jihar Bayelsa daga filin miƙa mulki a dandalin ‘Eagle’ jami’ai sun yi tantamar buɗe wa Jonathan ɗakin zaman alfarma na Shugaban Ƙasa, don a lokacin ba shi ne shugaban ba.

Wannan tafiya ta zama damarsa ta ƙarshe a lokacin ta amfani da jirgin Shugaban Ƙasa da na mai saukar angulu na Shugaban Ƙasa. Ko a can wajen tarben sa ma ba su gamu da wasu mutane, don tarar Jonathan ba, don bayan rasa mulkin; Abati ya ce, ba sa wuce su huɗu ke zama da Jonathan ba, don mutane sun ƙaura zuwa gidan sabon shugaban ƙasa. Wannan ba wani sabon abu ba ne idan mun duba yadda wasu tsoffin gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi ke rasa tagomashi bayan wasu shekaru.

Taron motoci da ’yan sanda da ke rakiya su na banke mutane haka kurum, don rashin sanin ya kamata a kan titina, sai ya ɗauke cak. Haƙiƙa akwai lokacin da na gaisa da wani mutumi, inda bayan mun yi musabaha, sai a ka ce min ai shi ne wane, tsohon gwamnan jiha kaza!

A nan zan shiga gadan-gadan taken rubutun nan na wannan mako kan ƙasar Libya da idan an yi sa’a za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasar a watan gobe. Ɗan tsohon shugaban Libya Marigayi Muammar Ghaddafi, wato Saiful Islam, ya ayyana shiga neman takarar shugabancin ƙasar.

Duk da akwai jerin masu neman takara, amma kafafen labarai sun fi mayar da hankali ga Saiful Islam, don kasancewarsa ɗan Marigayi Muammar Ghaddafi kuma wanda ya yi nisan kwana ba a halaka shi ba duk da yadda guguwa ta so gamawa da sauran ’yan uwansa bayan kisa mai ban takaici ga mahaifin nasa da ma wulaƙanta gawar mahaifin, inda har wasu ke zuwa ɗaukar hoto da gawar, inda daga ƙarshe ba a ba wa gawar martabar jana’iza yadda ya dace kamar ta tsohon shugaba mai tasiri irin Ghaddafi ba.

Gaskiya labarin ya na da ban juyayi da nuna shugabanci ba ya dauwama a hannun bani adama kuma ko ya dauwama kamar misalin yadda sarakuna kan iya zama kan sarauta har zuwa mutuwarsu, za ka ga da zarar an naɗa sabon sarki sai a cigaba da busa algaita a na shagali da yin kirarin sabon sarki inda daga nan an manta batun tsohon sarki da a ke yi wa kirari da toron giwa mai ban tsoro, gurnanin zaki da sauran zuga irin ta ‘yan sha miya na fada. Abun da zai taya mutum zama mai mulki ne ko marar mulki a rayuwa da bayan rayuwa shi ne halin sa mai kyau ko mummuna.

Hukumar zaɓen Libya ta tsayar da ranar 24 ga watan gobe a matsayin ranar zaɓen shugabancin ƙasar ta Afurka ta Arewa. Saiful Islam na cikin na kan gaba a jerin masu neman shugabancin ƙasar da su ka haɗa da kwamandan gwagwarmaya na gabashi Khalifah Haftar, firaminista Abdulhamid Al-Dheibah da kakakin majalisa Aguila Saleh.

An ga Saiful Islam da farin rawani da farin gemu ya na cika takardar tsayawa takara a garin Sebha na kudanci. Duk da mara baya ga gudanar da zaɓen da ƙasashen duniya ke yi, ba tabbas na lalle zai iya samun nasarar gudana ba.

Ganin tsawon lokaci na rasa mulkin Muammar Ghaddafi da a ka yi wa kisan gilla a 2011, masu sharhin siyasa na ganin tabbas in Saiful Islam zai iya tara jama’a da za ta mara ma sa baya kamar sauran ‘yan takarar. Ko banza Khalifa Haftar ya so ya kifar da gwamnatin ƙasar inda sai da a ka yi ta ba shi haƙuri da ɗaukar matakan diflomasiyya. Har ƙasashe Haftar yake zuwa inda ya gana da irin shugabannin larabawa da a ke ya yi yanzu wato Abdelfatah Alsisi na Masar.

A wannan lokaci in ba don tsoma bakin shugaba Raceb Tayyeb Erdoan na Turkiyya ba da tura sojojin Turkiyya Libya, gaskiya da Haftar ya hambare gwamnati da ƙarfin bindiga. Ko a yanzu Libya ba ta da tabbas, don tun kisan gilla ga Ghaddafi, ƙasar ta auka rabuwar kawuna da samun ƙungiyoyin gwagwarmaya na sassa inda kowanne ke yunƙurin kare ɓangaren da ya ke a ƙasar.

Ko ‘yan Libya sun yi nadama ko ma ba su yi nadama ba, ƙasarsu ta daina ba wa sauran ‘yan Afurka sha’awa. Musamman labarun da kan sa a tuno Libya su ne na mutanen da ke yunqurin tsallakawa turai da a kan cafke su da gana mu su azaba a sansanonin gwale-gwale a ƙasar.

Irin wadannan ‘yan Afurka da nahiyarsu ba ta ishe su walwala ba ko talauci ya takura su, ba su da alamar daddara daga neman kutsawa turai ta bin ƙasar Libya. Ga dai hatsari iri-iri da ke ƙunshe da kasadar har ma ba yiwuwar rasa rai, amma ina sai ka ji labarin an samu tawaga ta kunduma teku don neman shiga turai.

A nan za mu zuba ido kan Libya idan Allah ya kai mu wata mai zuwa, don ganin shin Ghaddafi ya mutu, Ghaddafi ya dawo?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *