A wani rahoto daga wani bincike da aka buga a makon da ya gabata an nuna cewa, aƙalla mutane 305 ne suka mutu yayin da mutane 449 suka samu munanan raunuka ta hanyar ruftawar benaye 83 a Nijeriya tun daga shekarar 2013, wanda ya kasance ba wai kawai abin damuwa ba ne amma kuma abin takaici ne.
Binciken da wata jarida ta ƙasa ta gudanar ya bayyana cewa, alƙaluman sun nuna ƙarara ga kafafen yaɗa labarai, domin da yawa ba a taɓa jin labarinsu ba. Ya ce, har yanzu Legas ce cibiyar rugujewar gine-gine a Nijeriya inda aka samu rahoton rahoton rugujewar gine-gine 50 tsakanin shekarar 2013 zuwa 2019. Gine-ginen sun sun haɗa da mashahuran cocin ‘Synagogue Church of All Nations’ (SCOAN), wanda rugujewarsa ya yi sanadin mutuwar mutane 115 tare da jikkata wasu sama da 131.
Al’ummar jihar Legas cibiyar kasuwancin Nijeriyar dai ta tsinci kai cikin ruɗani sakamakon wannan ibtila’in. Koda a shekara ta 2019 ma dai an samu afkuwar irin wannan ibtila’in, inda wani dogon benen ya faɗa kan wata makaranta tare da kashe ɗalibai kimanin 20 da kuma jikkata wasu da dama. Hukumomi a Nijeriya na danganta yawaitar rushewar gine-gine da rashin bin tsarin gini da ma rashin ingancin aiki.
Haka kuma an samu wasu ƙararraki a babban birnin tarayya (FCT), Kwara, Ogun, Ondo, Imo, Anambra, Abia, Ribas, Benue, Taraba, da Kano. Abin takaici, waɗannan bala’o’i ba su sa mutane sun hankalta ba wajen ganin yadda za a samar da ƙwaƙƙwaran matakai don dakatar da ci gaba da aukuwar hakan.
A cewar rahoton, masana sun danganta bala’o’in da kuskuren ɗan adam ciki har da gazawar da injiniyoyi suke yi na mutunta tsare-tsaren gini da ƙayyadaddun bayanai. An gano cewa, da yawa daga cikin injiniyoyin gine-ginen ma na bugi ne waɗanda ba ƙwararru ba.
Har ila yau, har ya zuwa yau ba a samu wani shaidadden hukunci na mutanen da ake zargin suna da hannu a cikin rugujewar ginin ba yayin da ake da shakku kan biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa. Majiyoyi sun ce yawancin masu ginin suna haɗa baki da jami’an tilasta yin aiki mai inganci don tafiya ba tare da hukunta su ba.
Rahoton ya ce, an samu rugujewar gine-gine guda 25 a shekarar 2021, 27 a shekarar 2020, 12 a shekarar 2019, biyu a shekarar 2018 da kuma takwas a shekarar 2017. A shekarar 2013, an samu rugujewar gidaje guda 7 sannan kuma an samu ƙararraki biyu a shekarar 2014. Ba a samu rahoton rushewar gini ba a cikin 2015, amma an rubuta biyu a cikin 2016.
Wani sabon lamari da ya faru a hanyar Gerald, Ikoyi, Legas makonni biyu da suka gabata, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 45, tare da jikkata da dama. Duk da cewa gwamnatin jihar Legas ta kafa kwamitin bincike, har yanzu ba ta bayyana binciken ta ga jama’a ba.
A halin yanzu, masana masana’antar gine-gine sun damu game da sabon abin da ya faru, suna kwatanta shi a matsayin mai ban tsoro. Emmanuel Chukwunonye Madu, Injiniya kuma babban jami’in gudanarwa na ‘Shungrila Estates Limited’, ya ce, yadda ake gudanar da ayyukan gine-ginen na haifar da gazawa ko rugujewa.
“Gini yana rugujewa lokacin da aka lalata daidaitattun hanyoyin, ko dai a lokacin ƙira ko gini,” inji shi.
Ya ba da shawarar cewa, ya kamata a gudanar da isasshen kulawa da himma ta hanyar ƙwararru a kan kowane gini kuma a kowane mataki na ci gaba.
“Amma maganin shi ne kafa ingantaccen tsarin kulawa a duk faɗin ƙasar, wanda ya haɗa ƙwararrun ma’aikata don duka matakan ƙira da gine-gine. Dole ne gwamnati ta yi aiki da gaske kuma ta yi aiki tare da qwararru wajen fannin gine-ginen ƙasar don samar da ingantaccen tsarin sa ido ba tare da takaici da munanan ayyuka ba. A na iya yin hakan,” inji shi.
Shugaban Cibiyar Nazarin Adadin Jama’a ta Nijeriya (NIQS), Alhaji Mohammed Abba Tor, ya buƙaci ’yan Nijeriya su ba ƙwararru damar gudanar da ayyukansu a koyaushe. Ya kuma jaddada cewa, yin amfani da kaya marasa inganci wajen aikin gini ne ke haddasa yawaitar rugujewar gine-gine a ƙasar.
Ya kuma ce, amfani da ingantattun kayayyaki da isassun kayan aiki shine mabuɗi don samar da gine-ginen da za su iya jure kowane yanayi da lokaci.
“Yin amfani da kaya masu inganci a daidai adadin ya zama dole. Shi ya sa amfani da ƙwararru a fanni gini tun daga matakin zane har zuwa matakin kammala shi ne mafita ne wajen kawo ƙarshen rugujewar gine-gine,” inji shi.
Shugaban Majalisar Dokokin Injiniyoyi a Nijeriya (COREN), Injiniya Ali Rabiu, ya ce, majalisar ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin binciko asalin abin da ya faru a Ikoyi.
“Bayan rushewar, mun gudanar da shawarwari da dama da masu ruwa da tsaki a fannin gine-gine. Daga baya, a madadin Majalisar, na kafa kwamitin bincike na musamman na COREN akan ginin da ya ruguje mai hawa 21 a Ikoyi, jihar Legas,” inji shi.
“Wannan yana bin sashe na 1 (1) (h) na Injiniyanci (Rijista, da dai sauransu), gyara Dokar, 2018, wanda ke ba da ikon COREN don bincika gazawar injiniyoyi,” inji wani ɓangare na sanarwar.
Tsohon shugaban Cibiyar Gine-gine ta Nijeriya (NIOB), Kunle Awobodu, ya ce, dole ne a yi abubuwan da suka dace tun daga farko har zuwa ƙarshen aikin ginin.
Abin takaici ne a yayin da al’ummar qasar ke fama da ɗimbin matsalolin rashin tsaro da suka haɗa da rikicin Boko Haram, ’yan fashin daji, masu garkuwa da mutane, fyaɗe, da dai sauransu da ke ci gaba da laqume rayukan ’yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba, za a iya ƙoƙarin ganin an magance wannan bala’i ta rushewar gini.
Don haka muna kira ga gwamnati a dukkan matakai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar gine-gine da su farka da nufin samar da ingantacciyar hanyar da za ta daƙile rugujewar gine-gine a ƙasar nan. Masu laifin rugujewar ginin Ikoyi na baya-bayan nan su fuskanci fushin doka domin su zama darasi ga wasu.