Zamfara: Jirgi ya kai hari ne bayan isowar ’yan bindiga kasuwar Tumfa – Shaidu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da ce-ce-ku-ce ke ci gaba da ƙaruwa kan harin saman da ya halaka mutane da dama a kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, wani mazaunin yankin ya bayyana cewa jirgin yaƙin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ya kai harin ne jim kaɗan bayan isowar ’yan bindiga kasuwar.

ƙauyen Tumfa, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, yanki ne da tattalin arzikinsa ya dogara da noma da kasuwanci. Kasuwar yankin na karɓar baƙuncin ‘yan kasuwa daga Nijar da kuma jihohin Zamfara da Katsina, musamman daga Shinkafi da Jibiya.

Majiyoyin yankin sun yi iƙirarin cewa sama da fararen hula 117, galibinsu mata da yara, sun rasa rayukansu yayin da wasu fiye da 100 suka jikkata. Sai dai rundunar sojin Nijeriya ta musanta wannan adadi a ranar Laraba.

Sai dai sanatocin Arewa sun buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci ga waɗanda suka rasa rayukansu ba tare da wani laifi ba.

Da yake zantawa ta wayar tarho da jaridar Blueprint a ranar Laraba, wani mazaunin yankin mai suna Malam Haruna Lawali Tumfa ya ce harin ya afku ne yayin da ‘yan bindiga ke cikin kasuwar.

“A lokacin da aka kai harin, ’yan bindigar suna cikin kasuwa, kuma da dama daga cikinsu sun mutu sakamakon harin,” inji shi.

“Amma zuwa yanzu mun rasa sama da mutum 117, yawancinsu mata ne da yara, yayin da fiye da mutum 100 suka jikkata.”

Ya bayyana cewa, ’yan bindigar kan shiga kasuwar ne a ranakun kasuwa domin sayar da dabbobi tare da sayen kayan abinci.

“A wannan rana jirgin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ya iso ne jim kaɗan bayan zuwan ‘yan bindigar sannan ya jefa bama-bamai a dukkan kasuwar,” inji shi.

Malam Tumfa ya roƙi gwamnatin tarayya ta tura ƙarin jami’an tsaro yankin saboda yadda rayukan jama’a ke ci gaba da kasancewa cikin haɗari sakamakon yawaitar ’yan bindiga.

Haka kuma ya yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da ta tallafa wa waɗanda suka jikkata, yana mai cewa da dama daga cikinsu ba su da ƙarfin biyan kuɗin magani.

“A yanzu haka mun kai sama da mutum 40 Asibitin ƙwararru na Shinkafi, yayin da wasu 40 kuma aka kai Gusau bisa la’akari da tsananin raunukan da suka samu. Waɗanda raunukan nasu ba su yi tsanani ba an sallame su,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin yankin, Garba Ibrahim Mashema, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa yana da wahala a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu.

“Kowa na zuwa kasuwa, mazauna yankin da kuma ‘yan bindiga. Jama’a na cikin mawuyacin hali saboda babu abin da za su iya yi,” ya bayyana.

Da take mayar da martani kan lamarin, Hedikwatar Tsaro ta ƙasa (DHƙ) ta ce babu wata hujja tabbatacciya da ke nuna cewa fararen hula sun mutu a harin.

Mai magana da yawun DHƙ, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce an gudanar da harin ne bisa ƙa’idojin dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, kuma an kai shi ne kan wani taron manyan jagororin ‘yan ta’adda da aka tabbatar da faruwarsa ta hanyar bayanan sirri daga mabambantan hanyoyi.

“Babu wata hujja mai ƙarfi ko bincike mai zaman kansa da ya tabbatar da mutuwar fararen hula,” inji Onoja.

Ya ce, yanayin aikin ya sanya samun cikakken bayani nan take ya zama da wahala, amma binciken bayan harin ya nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama.

Kakakin DHƙ ya ƙara da cewa rundunar sojin Nijeriya na ci gaba da ƙoƙarin gudanar da hare-hare cikin tsanaki domin rage asarar rayukan fararen hula tare da ƙara matsa lamba kan ƙungiyoyin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.

Ya kuma yi gargaɗin cewa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba na iya kawo cikas ga yaƙin da ake yi da ta’addanci tare da jefa al’umma cikin fargaba.

A martaninsu kuwa, sanatocin Arewa sun buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike kan harin.

Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa (NSF), Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja.

ƙungiyar ta buƙaci a gudanar da bincike mai zurfi, gaskiya da adalci kan yadda harin ya faru.

Sanatocin sun ce iyalan waɗanda suka mutu sun cancanci sanin gaskiya tare da samun adalci da diyya.

“Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutum 72 sun rasa rayukansu yayin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum,” sanarwar ta ce.

“Hotunan ɓarnar da aka gani, asarar rayukan da ba za a iya gane gawarwakinsu ba, da kuma raɗaɗin da iyalai ke ciki yayin binne ‘yan uwansu a rana guda, abin takaici ne kuma ba abin amincewa ba ne.”

Sanatocin sun jajanta wa iyalan da suka rasa ‘ya’yansu, iyaye da masu ɗaukar nauyin gidajensu, tare da yi wa waɗanda ke jinya a Zurmi, Shinkafi da Asibitin ƙwararru na Yariman Bakura da ke Gusau addu’ar samun lafiya.

Sun ce yankin Arewa da jihar Zamfara sun sha wahala sosai sakamakon matsalar tsaro, don haka wajibi ne shugabanni su tabbatar cewa fararen hula ba su zama waɗanda za su biya mafi girman farashi ba yayin yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda.

By ukarofi