2027: Gwamna Makinde ya ayyana tsaya wa takarar Shugaban ƙasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban ƙasar Nijeriya a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa ƙasar na buƙatar gaggawar sake fasalin siyasa da tattalin arziki.

Makinde ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wani gagarumin gangami da aka gudanar a Ibadan domin ƙaddamar da haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyar PDP da jam’iyyar Allied Peoples’ Movement (APM).

Ya ce matsalolin da Nijeriya ke fuskanta na buƙatar ƙarin shiga da jama’a za su yi cikin harkokin mulki, tare da haɗin kai mai ƙarfi tsakanin jam’iyyun adawa.

Gwamnan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su daina zama masu kallo kawai, su shiga cikin harkokin shugabanci domin ceto ƙasar daga halin da take ciki.

Ya jaddada cewa halin da Nijeriya ke ciki yanzu na buƙatar haɗin kai da matakan gaggawa daga kowa.

Makinde ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da su ƙara haɗa kai domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da samar da kyakkyawar hamayya a ƙasar nan.

Gwamnan ya bayyana haɗin gwiwar PDP da APM a matsayin “babbar kawance” da aka kafa domin tsayar da ‘yan takara a dukkan matakan zaɓe daga shugaban ƙasa har zuwa majalisun jihohi.

A cewarsa, haɗin gwiwar na da manufar sake farfaɗo da jam’iyyun adawa tare da ƙarfafa gasa a siyasar Nijeriya gabanin zaɓen 2027.

A ƙarshe, Makinde ya bayyana a hukumance cewa zai nemi kujerar Shugaban ƙasar Nijeriya a zaɓen 2027, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa zai zama wata kafa ta kawo sauye-sauye masu anfani ga ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi