WhatsApp ta magantu kan yadda waɗanda ba su da lambar masu manhajar ke iya duba ‘status’

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin WhatsApp ya mayar da martani bayan wasu masu amfani da manhajar sun koka a kafafen sada zumunta cewa lambobin waya da ba su ajiye a cikin wayoyinsu suna iya ganin Status ɗinsu, lamarin da ya sake tayar da muhawara kan tsaron sirri a dandalin.

Masu amfani da dama sun bayyana damuwa a shafin ɗ, inda suka ce lamarin ya ba su mamaki tare da jefa su cikin rashin jin daɗi, suna tambayar ko sabuwar matsala ce ta saituna ko kuma wata tangarɗa ce ta fasaha.

Wasu daga cikin masu amfani da shafin sun nuna damuwa cewa lamarin na iya shafar yadda tsarin sirrin Status ke aiki, tare da neman WhatsApp ta yi ƙarin bayani a fili.

Wani mai amfani da shafin, @JustKingss, ya bayyana cewa ba daidai ba ne mutanen da ba a ajiye lambobinsu ba su riƙa ganin Status ɗin mutane. Ita ma wata mai amfani da shafin mai suna @ms___dale ta tambayi ko hakan yana nufin wasu ma suna iya ganin nata Status ba tare da saninta ba.

Sauran masu amfani da shafin sun kuma nuna fargaba kan yadda iyakar ganin bayanan sirri ta fara raguwa, inda wasu suka ce al’amarin ya sa tsarin kariyar sirri ya zama tamkar ba shi da ƙarfi kamar yadda yake a baya.

Sai dai a martanin da ta fitar, WhatsApp ta tabbatar wa masu amfani cewa babu wani sauyi da aka yi a tsarin tsaron sirrinta.

Kamfanin ya ce saƙonnin sirri, kira da kuma Status na masu amfani har yanzu suna ƙarƙashin kariyar “end-to-end encryption”, yana mai jaddada cewa tsarin tsaro na asali bai sauya ba.

“Ana ci gaba da kare saƙonninku, kiraye-kirayenku da Status ɗinku ta hanyar tsarin end-to-end encryption, kuma babu wani sauyi da aka yi a wannan ɓangare,” inji WhatsApp a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X.

By ukarofi