Yadda jami’in banki ya tona mu’amalar asusun Malami ga NFIU

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wani jami’in kula da bin ƙa’idoji na Bankin Zenith Plc, Mashelia Bata, ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa bankin ya kai rahoton wata mu’amala da ake zargi zuwa Hukumar Bayanan Sirrin Kuɗaɗe ta Nijeriya (NFIU) dangane da wasu kuɗaɗe da suka shiga wani asusun da ake alaƙantawa da tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami.

Jami’in ya bayyana hakan ne yayin shari’ar da ake yi wa Malami tare da matarsa da ɗansa kan zargin halasta kuɗaɗen haram da suka kai naira biliyan 8.7.

Ana tuhumar waɗanda ake ƙara da laifuka guda 16 da suka shafi zargin halasta kuɗaɗen haram, inda dukkansu suka musanta zarge-zargen da ake musu.

A cewar wata sanarwa da Hukumar EFCC ta fitar, lauyan waɗanda ake ƙara, Adebayo Adedeji, ne ya yi wa shaidar tambayoyi yayin zaman kotun.

Yayin amsa tambayoyi, jami’in bankin ya amince cewa kuɗaɗen da suka shiga asusun sun bi ƙa’idojin Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Sai dai ya ce duk da bin ƙa’idojin, bankin ya ga dacewar kai rahoton mu’amalar ga NFIU saboda yadda ake samun maimaituwar shigar kuɗin cikin tsarin da ya janyo zargi.

A yayin zaman kotun, lauyan EFCC, Jibrin Okutepa, ya buƙaci shaidar ta yi ƙarin bayani kan ma’anar Suspicious Transaction Report (STR) wato rahoton mu’amalar da ake zargi.

Sai dai lauyan masu ƙara, Adedeji, ya nuna rashin amincewa da tambayar, yana mai cewa kalmar ba ta da ruɗani da zai sa sai an yi ƙarin bayani.

Da yake martani, Okutepa ya ce Sashe na 215(3) na Dokar Shaidu bai hana shi sake tambayar shaida karin bayani ba, tare da roƙon kotu ta ba da damar yin tambayar.

Mai shari’a, Justice Joyce Abdulmalik, ta yi watsi da ƙorafin da lauyan masu ƙara ya gabatar, tare da bai wa shaidar damar amsawa.

Da yake ƙarin bayani ga kotun, jami’in bankin ya ce doka ta wajabta wa bankuna kai rahoton duk wata mu’amala mai maimaituwa ko wadda ake zargi ga NFIU.

“Duk wata mu’amalar kuɗi da aka lura tana da tsarin maimaituwa ko abin zargi, wajibi ne a kai rahotonta ga NFIU,” inji shaidar.

Bayan kammala bayar da shaidarsa, an sallami Mashelia Bata daga akwatin shaida.

Daga nan sai Mai shari’a Abdulmalik ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 22 ga watan Mayu domin ci gaba da shari’ar.

By ukarofi