Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS), Bashir Adeniyi, ya tabbatar da cewa wasu ‘yan ta’addan Lakurawa sun kashe jami’an hukumar guda biyu a jihar Kebbi.
Adeniyi ya bayyana hakan ne ranar Laraba a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara, inda ya ce jami’an sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile hare-haren ‘yan ta’addan da misalin ƙarfe 3 na dare.
Ya bayyana sunayen jami’an da suka rasu da ASC Bamigboye da DSC Dom.
Babban jami’in na Kwastam ya bayyana hakan ne yayin gabatar da muƙalar buɗe taro a taron ƙasa da ƙasa karo na huɗu da Tsangayar Sadarwa da Kimiyyar Bayanai ta Jami’ar Ilorin ta shirya, tare da haɗin gwiwar Tsangayar Nazarin Harsuna ta Jami’ar Rudn da ke ƙasar Rasha.
A cewarsa: “Da safiyar yau Laraba, jami’ai biyu na Hukumar Kwastam ta Nijeriya sun sadaukar da rayukansu yayin da suke kare ƙasa daga barazanar ‘yan ta’addan Lakurawa a jihar Kebbi.”
Adeniyi ya nuna alhininsa kan lamarin, yana mai cewa baya ga sojoji, jami’an Kwastam su ne “garkuwa ta ƙarshe” wajen yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin.
Ya ƙara da cewa da bai riga ya iso Ilorin domin halartar taron ba, da wannan mummunan labari ya sa ya soke tafiyarsa.
Sannan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan jami’an da suka rasu, tare da tabbatar da cewa wannan hari ba zai hana hukumar da jami’anta ci gaba da gudanar da ayyukansu na kare ƙasa ba.
A ƙarshe, mahalarta taron sun tsayar da minti ɗaya domin girmama jami’an da suka rasa rayukansu.
