Hajjin 2026: Nuru Khalid ya buƙaci maniyyatan Nijeriya su yi haƙuri da jigilar NAHCON a Makkah

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Nuru Khalid, ya buƙaci maniyyatan Nijeriya da su ƙara haƙuri tare da nuna fahimta ga hukumomin aikin Hajji yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da jin dazinsu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Sheikh Khalid ya yi wannan kira ne ranar Alhamis yayin da yake yi wa maniyyata daga Babban Birnin Tarayya Abuja da Jihar Oyo jawabi bayan isowarsu Makkah daga Madinah.

Malamin ya bayyana cewa gudanar da ibadar Hajji, musamman a lokacin sanya harami, na buƙatar juriya da haƙuri sosai daga mahajjata.

Ya ce akwai buƙatar sauyin hali da fahimtar juna, yana mai jaddada cewa ba domin yin addu’ar kai kaɗai aka je aikin Hajji ba, har ma da yi wa Nijeriya addu’ar zaman lafiya da ci gaba.

Sheikh Khalid ya yaba wa Hukumar Alhazai ta ƙasa bisa irin hidimomin jin daɗi da take samar wa maniyyatan Nijeriya.

A cewarsa, abincin da ake bai wa alhazai yana da inganci tare da wadatarwa, yayin da masaukan da aka tanada suke kusa da Masallacin Harami.

Sai dai ya roƙi NAHCON da ta ƙara ƙoƙari wajen tattaunawa da hukumomin Saudiyya domin bai wa maniyyatan Nijeriya damar ziyartar Rawda, wato wurin da kabarin Annabi Muhammad (SAW) yake.

Ya ce akwai maniyyata da dama, har da shi kansa, waɗanda suka je aikin Hajji sau da dama amma ba su samu damar shiga Rawda ba.

Shi ma mai taimaka wa Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmi ta Jihar Adamawa, Abdullahi Barkindo, ya yabawa NAHCON bisa yadda take kula da jin daɗin maniyyatan Nijeriya.

Barkindo ya yi wannan jawabi ne yayin isowar maniyyatan Adamawa Makkah daga Madinah. Ya ce, duk da cewa ya je Saudiyya tun farko a matsayin tawagar gaba, hukumar ta samar masa da masauki a Madinah tare da kula da su yadda ya kamata.

A cewarsa, ana ba su abinci sau biyu a rana, kuma abincin yana da gina jiki da inganci.

Haka kuma, mamba a Hukumar Jin Daɗin Alhazai Musulmi ta Jihar Bauchi, Muhammad Ibrahim, ya bayyana cewa jami’an NAHCON suna aiki tare da maniyyata cikin mutunci da haɗin kai domin tabbatar da jin daɗinsu.

Ya ce jami’an hukumar suna nuna ƙwazo, biyayya da kuma haɗin kai wajen gudanar da ayyukansu a Saudiyya.

By ukarofi