Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da Fadar Shugaban ƙasa sun shiga cacar baki kan furucin da ya yi cewa zai yi wa’adi guda ɗaya kacal idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na News Central, inda ya ce ko da an ɗora masa bindiga a kai ba zai zauna kan mulki fiye da shekara huɗu ba.
“Ina son zama shugaban ƙasa mai wa’adi ɗaya ne saboda samar da daidaito da kwanciyar hankali. Ko da an ɗora mini bindiga a kai, ba zan ƙara kwana ɗaya bayan shekara huɗu ba,” inji Obi a cikin bidiyon da ya karaɗe kafafen sada zumunta.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya kuma soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya, musamman batun karɓo bashi da tashin gwauron zabi na rayuwa, yana mai cewa Nijeriya ta shiga ɗaya daga cikin mafi tsananin matsalolin tattalin arziki a tarihinta.
Obi dai ya tsaya takarar shugaban aasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party, inda ya zo na uku bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.
Tun bayan zaɓen, Obi ya ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan jagororin adawa da ke yawan sukar manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu.
Sai dai cikin martanin da Fadar Shugaban ƙasa ta mayar, mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi watsi da alƙawarin na Obi, yana mai cewa tarihinsa na siyasa ya nuna rashin tsayawa kan magana.
“Idan har mutum zai yarda da alƙawarin Peter Obi na yin wa’adi ɗaya kacal, to zai iya yarda da komai,” inji Onanuga a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ.
Ya ce Obi ya taɓa yin mubaya’a ga jam’iyyar APGA lokacin da yake gwamnan jihar Anambra, amma daga baya ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP, kafin daga bisani ya koma wasu jam’iyyu daban-daban.
“Alƙawuran Peter Obi ba sa daɗewa. Daga ƙarshe ya bar APGA zuwa PDP, sannan ya ci gaba da yawo daga wannan jam’iyya zuwa wata,” inji shi.
Onanuga ya ƙara da cewa, sauye-sauyen siyasar da Obi ya riƙa yi a tsawon shekaru sun nuna cewa ba za a iya dogaro da kalamansa ba.
A cewarsa, “Ayyukansa ne suka nuna cewa kalamansa ba su da tabbas, domin alƙawuransa suna canzawa kamar yadda yake sauya jam’iyya.”
Rahotanni sun kuma ce Obi, wanda ya yi takara a 2023 ƙarƙashin Labour Party, daga baya ya shiga jam’iyyar NDC bayan ficewarsa daga haɗakar jam’iyyar ADC gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
