Zamfara: Sojoji sun halaka ƴan bindiga sama da 100 a Bukkuyum

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro sun yi nasarar halaka sama da ƴan bindiga guda 100 a wani luguden wuta ta sama da ƙasa a Jihar Zamfara, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An ƙaddamar da mummunan harin ne akan ƴan bindigar a Ƙaramar Hukumar Bukkuyum yayin harin sama da 400 daga cikinsu a dajin Makakkari.

Sojojin sama a jiragen yaƙi da suka yi aiki tare da sojojin ƙasa, sun tarwatsa sansanin ƴan ta’addar gabannin kashe waɗanda suka yi yunƙurin tserewa.

Ana ganin hakan a matsayin martani ga munanan hare-haren ƴan bindigan akan al’umma da jami’an tsaro musamman a watan da ya gabata a sassa daban-daban na jihar.

Kwanaki biyu gabannin farmakin sojojin, ƴan ta’adda sun kai wani hari mai muni a ƙauyen Adabka da ke Bukkuyum inda suka yi garkuwa da mutane da dama a yankin bayan halaka jami’an tsaro 13.

Wani bayanin sirri ya nuna cewa, maharan suna shirin kai wani hari ne a wani ƙauyen manoma, inda a yayin haka dakarun suka yi musu diran mikiya.

By Babaji