
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan ƙasar Burkina Faso su guda biyar a wani wurin haƙar ma’adinai da ke Jihar Zamfara State.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Maru Local Government Area, inda maharan suka kai hari suka tafi da mutanen zuwa cikin daji.
Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar ranar Asabar a lokacin da dandazon maharan suka kai farmaki a ƙauyukan Arafa da Gidan Dankande.
Jami’an tsaro sun ce ana cigaba da bincike da farautar maharan, domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Masanin a harkar tsaro Zagazola Makama ya ce al’amarin wani ɓangare ne na rashin jituwa da ake su tsakanin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ‘yan bindiga a Zamfara.
