
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fraministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya magantu game da barazanar farauta da halaka shi da Iran ta yi, yayin rikicin ƙasashen biyu ke cigaba da ƙamari.
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC), ta bayyana haka inda ta ci alwashin farauto jagoran Isra’ilan bayan jerin hare-haren ƙasar akan ababen harin Iran.
A sanarwar da IRGC ta fitar wa gidajen jaridun Iran, ta bayyana Netanyahu a matsayin babban mai laifi, sannan ta yi gargaɗin cewa Tehran za ta cigaba da ƙoƙarin ganin bayansa.
Hakan an zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗi a kafafen sada zumunta akan lafiya da wajen da Netanyahu yake, inda ake ganin ko an halaka shi a yaƙin.
Saidai, ana tsaka da haka ne Fraministan Isra’ilan ya bayyana a wani faifan bidiyo da ya wallafa ta kafar X yayin ake zargin an halaka shi, sai aka gan shi a ciki yana sayen shayi a wani shago tare da yin raha akan jita-jitar.
An ga Netanyahu na kuma nuna hannayensa biyu ga kyamara wajen yin shaguɓe akan zargin, inda ya ce “Na mutu…. ga ‘Coffe’.”
