
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin ‘yan barandar siyasa ne na tsagin jam’iyya mai mulki (APC), sun hargitsa wani wajen taro da aka shirya yi domin ƙaddamar da buɗe sakatariyar jam’iyyar ADC a Ƙaramar Hukumar Bakassi da ke Jihar Kuros-Riba.
Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun farmaki wajen ne a jiya Asabar, inda suka tarwatsa magoya bayan jam’iyyar da lalata rumfunan da aka kafa, kujeru, ansakuwa da wasu kayayyaki da aka shirya gudanar da taron da su.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar ta tabbatar da faruwar al’amarin ta bakin kakakinta, Sunday Eitopkah.
‘Yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike kan lamarin domin gano wadanda ke da hannu a harin tare da daukar matakan doka a kansu.
Hukumomin tsaro sun kuma buƙaci jama’a da su guji tada hankula tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
