‘Yan daba sun kai wa ɗan jarida hari saboda ya tsawatar musu kan rashin yin azumi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wasu gungun ‘yan daba sun ji wa wani ɗan jarida kuma mai aikin Hisbah, Idris Usman Alhassan rauni a jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta samu labarin cewa lamarin ya faru a Unguwar Kurna Tudun Bojuwa Titin Rufaidah a ƙaramar hukumar Fagge inda ƴan daban su ka jikkata Idris saboda ya ga su na share-shaye da tsakar rana yayin da ake azumin watan Ramadan.

Rahotanni sun nuna cewar ɗan jaridar ya tsallake rijiya da baya ne bayan da wani daga cikin ƴan daban da aka bayyana sunan sa da Yusuf Mai Ƙarfi ya yi yinƙurin caccaka masa wuka.

By ukarofi