Zan Kammala aikin hanyar Wuju-wuju kafin kwana 100 a ofis – Gwamna Abba

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya ba da tabbacin zai kammala aikin hanyar Wuju-wuju mai nisan kilomita 1.2 kafin ya cika kwana 100 a ofis.

Yusuf ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar gani da ido game da yadda aikin hanyar ke gudana.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a Kano a ranar Laraba.

Dawakin-Tofa ya rawaito Gwamnan na cewa, an ba da kwangilar aikin hanyar ne a lokacin wa’adin mulki na biyu na tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso.

Gwamnam ya ce, “Burina ya cika ganin cewa ni ma na ba da gudunmawata ga wannan aiki mai matuƙar muhimmanci na gina magudanan ruwa da hanya mai nisan kilomita 6.7 a kusa da Rafin Jakara- Kwarin Gogau.

“Gwamnatin da ta gabata ce ta yi watsi da aikin bayan mun tafi a 2015, kuma an assasa aikin ne domin daƙile tasirin sauyin yanayi a Kano,” in ji shi.

Daga nan, Gwamnan ya yi kira ga ɗan kwangilar kan ya yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da aikin ya kammala kafin cikarsa kwana 100 a ofis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *