Cire tallafin fetur: Gwamnatin Zamfara za ta raba kayan abinci

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada umurnin gaggauta raba kayan abinci a ƙananan hukumomi 14 da ke faɗin Jihar domin rage raɗaɗin wahalar da janye tallafin fetur ya jefa al’umma.

Wata sanarwa wacce mai magana da yawun gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa za a yi rabon kayan abinci ne duba da irin mawuyacin halin da al’umma ke ciki, kuma bisa ƙudurin gwamnatin Jihar na bin duk wata hanya ta sauƙaƙa wa jama’a.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin ta yi shiri mai kyau don tabbatar da cewa mabuƙata sun amfana da wannan tallafi.

Ya ce: “Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bada umurnin a gaggauta raba kayan abinci ga al’umma a matsayin agajin gaggawa don rage raɗaɗin halin da ake ciki sakamakon janye tallafin mai.

“Saboda irin halin tausayi na Gwamna Lawal ya sa, ya ce a fara da raba kayan abincin, cikin jerin hanyoyin da gwamnatinsa ke son bi don agaza wa al’umma.

“Ɓangare na farko na wannan agaji zai fara ne da rabon Shinkafa da Masara.

“Tuni dai an samar da hanyoyin yin wannan rabo sannan kuma an kafa kwamitin da zai ɗauki alhakin wannan aiki.

“Daɗin daɗawa, gwamnatin ta Zamfara ta yi amanna cewa wannan agajin na kayan abinci zai amfani al’umma, kafin sauran tallafin su biyo baya.”