
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Mai girma Mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya aika saƙon neman taimakon ƴan Nijeriya kan ƙaddamar da shirye-shirye da ayyukan Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya na mai cewa shugaban ƙasar na nufin al’umma da alkhairi.
Ya ce, jita-jita a wasu wurare na cewa Shugaba Tinubu na adawa da cigaban Arewa ko Musulunci ba haka ba ne, ya mai buga misali da cewa hakan da zai nuna yayin raba manyan muƙamai da Tinubu ya yi na ma’aikatu, hukumomi da ofisoshin wasu ɓangarori.
Shettima ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin tawagar ƴan jarida a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya ce, duk da cewa zanga-zanga wani ɓangare ne na ƴancin ƴan ƙasa, yin sa na da rashin amfani a cikin al’umma wanda hakan ka iya haifar da asara da dama wa mutane da ma ƙasa baki ɗaya.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, gwamnatinsu ta na da kyakkyawar manufa ta sauya rayukan al’ummar Arewa ta hanyar samar da ababan cigaba tare da ƙoƙarin magance matsalolin da ke addabar su.
Kaɗan daga cikin misalan da ya bayar su ne; samar da tsarin bayar da matsuguni ga waɗanda ibtila’in ta’addanci ya rutsa da su (RSPIC) da ƙirƙirar ma’aikatar bunƙasa harkokin kiwo, ya na mai cewa “kar mu gurɓata tunanin al’ummarmu waɗanda aka ba su bayanan da ba haka su ke ba na cewa shugaban ƙasa bai son Arewa”, inji shi.
“Ina son na jaddada wannan gaskiyar, kuma ina faɗin haka ne saboda na san matsayar shugaban ƙasa ga Arewa. Mutum ne mai kirki da adalci. Ya na son Arewa, sannan kuma ya na aikin gyara yankin” inji Shettima.
Game da al’amarin zanga-zanga, Shettima ya ce, yin gangami ba zai bayar da tabbacin samun cigaba a yankin ba, ya na mai roƙon al’umma su taimaka wa gwamnatin Tinubu wajen cimma burinsa na kawo cigaba a yankin Arewa.
Bugu da ƙari, ya roƙi ƴan jarida su cigaba da wayar da kan al’umma game da damanmaki da gwamnati ke bayarwa don inganta rayuwa da zamantakewarsu.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga ƴan Arewa su bai wa gwamnatin Tinubu goyon baya domin bunƙasa ayyukan cigaba a yankin nasu.
