Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Zamfara dake mulki a jihar ta musanta zargin da jam’iyyar APC tayi na ɗaukar nauyin ‘yan bangar siyasa da suka yi yunƙurin Kai hari gidan tsohon gwamna kuma ministan tsaro na jihar, Hon Bello Muhammad Matawalle da ke Gusau da kuma fasa rumbun ajiya mallakin Sanata Sahabi Ya’u a garin Kaura Namoda a yayin gudanar da zanga-zanga da aka yi ranar Alhamis a faɗin ƙasar.
Muƙaddashin shugaban jam’iyyar na jiha kuma shugaban ma’aikatan gwamna Dauda Lawal, Hon. Muktar Lugga ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Gusau ranar Juma’a.
Hon. Lugga ya bayyana zargin da APC ke yi wa PDP a jihar a matsayin yaudara, rashin tabbas da kuma rashin soki burutsu.
A cewarsa, batun wahala da ‘yan Nigeria ke ciki ya janyo zanga-zangar adawa da gwamnatin APC saboda haka bai kamata APC ta sanya siyasa a lamarin ba.
Ya kara da cewa, ya kamata jam’iyyar APC a jihar ta mayar da hankali kan yadda za a yi abubuwan da ake buƙata ta hanyar baiwa gwamnatin ƙasa shawara mai kyau a kan al’amurran da suka shafi jihar ba sanya siyasa a ciki ba.
“Batun siyasa ba a fara ba tukuna, ina ba jam’iyyar APC shawara a jihar da ta mayar da hankali kan batutuwan da suka dace da za su iya kawo sauye-sauye masu kyau ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a jihar maimakon yaudarar mutane da maganganun siyasa na ƙarya ”. Yace
Hon. Lugga yaci gaba da cewa, gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya domin bunƙasa jihar musamman kan matsalar rashin tsaro da samar da ababen more rayuwa.
Ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar da su kwantar da hankulansu da bin doka da oda don baiwa gwamnatin jihar damar bunƙasa jihar a ko yaushe.
