Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da sabon sanarwar tsaro ga ‘yan ƙasar yayin da aka fara zanga-zangar #EndBadGovernance a duk faɗin Najeriya. Ofishin ya soke duk wasu aikin biza tsakanin 1 zuwa 2 ga watan Agusta.
A cikin wata sanarwa an shawarci ma’aikatan da aikin su ba na mahimman ba da su kasance a gida don guje wa duk wani cikas da ka iya faruwa saboda zanga-zangar da akeyi faɗin ƙasar.
Sanarwar ta ce, rahotannin kafafen yaɗa labarai na nuna cewa ana sa ran masu zanga-zangar za su fara hallara a dandalin Eagles Square da ke Abuja daga tsakar safiya. A Legas, ana iya fara zanga-zangar da karfe 8:00 na safe ko 9:00 na safe kuma an gano wuraren da aka fi sani da Alausa Park, Park Freedom, da Peace Park nan za a hallara.
“Karin wuraren da za a yi zanga-zangar a Legas sun hada da Nahco Bus Stop (Titin Jirgin sama), Marwa Bus Stop, da Ikeja ƙasan gada.
“Akwai haɗarin hare-haren ta’addanci a Najeriya kuma ƙungiyoyin ‘yan ta’adda na iya amfani da damar da aka samu yayin zanga-zangar da za a iya yi a faɗin kasar don kai hare-hare.”
Don haka tawagar ta Amurka ta shawarci ‘yan ƙasar ta da ke Najeriya da su guji wuraren da ake gudanar da zanga-zanga, da gujewa cunkoson jama’a da kuma yin taka-tsan-tsan kafin su fita.
An kuma shawarci ‘yan ƙasar da su sanya ido kan kafafen yaɗa labarai na cikin gida don samun sabbin bayanai, da kiyaye bayanan sirri, da kuma tabbatar da jadawalin jirage tare da kamfanin jirginsu, idan suna da tsare-tsaren tafiye-tafiye da sake duba tsare-tsaren tsaronsu, kiyaye cajin wayoyinsu na hannu idan wani lamari na gaggawa ya faru da kuma dauke da shaidar da ta dace. .
“Sashen Ofishin Jakadancin na Abuja da Ofishin Jakadancin Legas za su bayar da rage ayyukan ba da agajin gaggawa na Amurkawa kawai. An soke dukkan ayyukan biza,” in ji sanarwar.
