Da Ɗumi-Ɗumi: Bayan rabuwa da Offor, Kano Pillars ta naɗa sabon koci

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ta naɗa Abdullahi Usman a matsayin sabon mai horar da ƴan wasanta.

Ƙungiyar wacce ta lashe gasar frimiyar Nijeriya sau huɗu, ta sanar da hakan ne a shafinta na ‘Facebook’.

Ta ce “Mu na farin cikin sanar da cewa mun cimma yarjejeniyar naɗa Usman Abdullahi a matsayin sabon kocinmu.”

Ƙwararren kocin ya yi aiki da manyan ƙungiyoyi a frimiyar Nijeriya da su ka haɗa da; Enyimba da Wikki Tourists.

Hakan nan, tsohon Mataimakin kocin Super Eagles ɗin ya taimaka wa Katsina United wajen haurowa gasar frimiyar shekaru biyu da su ka gabata.

By Babaji